Gwamnan jahar Zamfara ya yi ruwan miliyoyin akan wasu Sojojin Najeriya guda 10

Gwamnan jahar Zamfara ya yi ruwan miliyoyin akan wasu Sojojin Najeriya guda 10

Gwamnatin jahar Zamfara ta sanar da bada tallafin naira miliyan biyar ga wasu jaruman dakarun Sojojin Najeriya guda goma da suka samu rauni yayin da suke fafatawa da yan bindigan da suka addabi jahar Zamfara, a filin daga.

Legit.com ta ruwaito a yanzu haka an kwantar da Sojojin a cibiyar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya dake garin Gusau, babban birnin jahar Zamfara, inda ake basu kulawar da ta dace.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Yan bindiga sun aikata ma wani gwamnan Arewa danyen aiki a gonarsa

Gwamnan jahar Zamfara ya yi ruwan miliyoyin akan wasu Sojojin Najeriya guda 10

Gwamnan jahar Zamfara
Source: Facebook

Kamfanin dillancin labaru ta ruwaito Sojojin sun jikkata ne yayin da wasu gungun yan bindiga suka kai musu harin kwantan bauna a tsakiyan dajin Dumburum dake cikin karamar hukumar Zurmi ta jahar Zamfara dake da iyaka da kasar Nijar.

A yayin wannan karan batta da aka kwasa tsakanin dakarun rundunar Sojan kasa ta Najeriya tare da hadin gwiwar dakarun Sojojin kasar Nijar da kuma yan bindiga a gefe daya, an samu asarar rayuka a dukkanin bangarorin, lamarin ya faru ne a ranar 28 ga watan Disamba.

Da yake mika cakin kudin ga marasa lafiya, kaakakin majalisar dokokin jahar Zamfara, Alhaji Sunusi Rikiji ya bayyana cewa gwamnatin jahar Zamfara ta yanke shawarar tallafa ma Sojojin ne don rage ma iyalansu radadin halin da suka shiga.

“Na mika muku tallafin naira dubu dari biyar biyar (N500,000) ga kowanne Soja cikin Sojoji goma dake aka kwantar a wannan asibiti a madadin gwamnan jahar Zamfara, Gwamna Abdul Aziz Yari.

“Dama gwamnatin jahar ta dauki nauyin biyan kudaden asibitinsu gaba daya, tare da ciyar dasu kyauta daga aljihunta, kuma tuni muka mayar da kwamandan tawagar Sojojin da aka kai ma hari, Kyaftin Danjuma zuwa babban asibiti ta kasa dake Abuja, kuma mu zamu biya.” Inji shi.

Daga karshe kaakaki Rikiji, wanda shine shugaban kwamitin kulawa da mutanen da rikicin jahar Zamfara ya shafa, ya jinjina tare da yabawa kokarin fa Sojoji suke yi na kawo karshe ayyukan yan bindiga a jahar, da ma sauran hukumomin tsaro.

A wani labarin kuma, Gwamna Abdul Aziz Yari ya halarci sallar jana’izar da aka yi ma Sojojin kasar Nijar su biyar da aka kashe a yayin samamen da yan bindigan suka kai, sa’annan ya baiwa iyalansu tallafin naira miliyan takwas da dubu dari biyar (N8,500,000).

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel