An kori 'yan sanda hudu saboda satar zunzurutun kudi 350,000cfa

An kori 'yan sanda hudu saboda satar zunzurutun kudi 350,000cfa

- Hukumar 'yan sandan Najeriya ta kori wasu jami'anta hudu da suka yiwa wani dan kasuwa, Theodore Ifunanya fashi

- Jami'an sune Victor Amiete, Saja Gbemunu Samuel, Saja Afolabi Oluwaseun da Kofur Adigun Omotayo

- An yanke shawarar korar 'yan sandan ne bayan Mr Theodore ya shigar da kara kuma an kafa kwamtin bincike da ta tabbatar da laifinsu

Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta kori wasu jami'an ta hudu da aka samu da laifin yiwa wani dan Najeriya mazaunin kasar Togo satar N350,000 cfa . An gano cewa an bukaci mataimakin Sufeta Janar 'yan sanda mai kula da Zone 2, Lawal Shehu ya sallami daya daga cikin 'yan sandan mai mukamin sufeta.

Yan sandan hudu, Victor Amiete, Saja Gbemunu Samuel, Saja Afolabi Oluwaseun da Kofur Adigun Omotayo sun karbi kudin ne daga hannun Mr. Theodore Omotayo.

An kori 'yan sanda hudu saboda satar zunzurutun kudi 350,000cfa
An kori 'yan sanda hudu saboda satar zunzurutun kudi 350,000cfa
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Dakarun Soji sunyi nasarar kashe mata 'yan kunan bakin wake uku

Jami'in hulda da 'yan sanda na Legas, CSP Chike Oti ya ce rundunar ta gudanar da bincike sannan ta tabbatar da cewa 'yan sandan sun aikata laifin hakan yasa aka bayar da umurnin korarsu daga aiki.

Oti ya ce kwamishinan 'yan sanda na jihar Legas, Imohimi Edgal ya bayar da umurnin korar jami'an masu kananan mukamai, Saja Ggemunu Afolabi, Saja Afolabi Oluwaseun da Kofur Adigun Omotayo. Sannan ana jiran amincewar ASP na Zone 2 domin korar Amiete.

"Idan ba a manta ba, a ranar 26 ga watan Disamba ne hukumar 'yan sandan ta bayar da sanarwar fara bincikar wasu jami'anta da ake zargi da saba dokar aiki yiwa wani Ifunanya Theodore fashi a yayin da ya ke hanyar zuwa gida kirsimeti.

"Sakamakon binciken da kwamishin 'yan sanda ya saka ayi ne ya tabbatar cewa 'yan sandan sun aikata laifi da bai dace ba kuma aka hukunta su."

A cewar Oti, wannan hukuncin da aka yanke zai zama izina ga sauran jami'an hukumar da su gudanar da ayyukansu a bisa ka'ida.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel