Aliyu Aminu: An kara gano wani matashin soja da ya mutu a sabon harin Boko Haram, hotuna

Aliyu Aminu: An kara gano wani matashin soja da ya mutu a sabon harin Boko Haram, hotuna

An bayyana rasuwar wani matashin soja mai suna Aliyu Aminu daga cikin jami'an tsaro 13 da mayakan kungiyar Boko Haram suka kashe a sabon harin kwanton bauna da suka ranar Litinin.

Sojoji 11 da jami'an 'yan sanda 2 ne suka rasa ransu bayan sun fada tarkon harin kwanton bauna da mayakan suka kafa a kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.

Duk da dakarun sojin sun mayar da martani ga harin na mayakan kungiyar Boko Haram, Aliyu, tare da wasu ragowar sojoji 11 da jami'an 'yan sanda 2 sun rasa ransu yayin musayar wuta.

Aliyu Aminu: An kara gano wani matashin soja da ya mutu a sabon harin Boko Haram, hotuna
Marigayi Aliyu Aminu
Asali: Facebook

Aliyu Aminu: An kara gano wani matashin soja da ya mutu a sabon harin Boko Haram, hotuna
Marigayi Aliyu Aminu
Asali: Facebook

Aliyu Aminu: An kara gano wani matashin soja da ya mutu a sabon harin Boko Haram, hotuna
Aliyu Aminu
Asali: Facebook

Aliyu Aminu: An kara gano wani matashin soja da ya mutu a sabon harin Boko Haram, hotuna
Marigayi Aliyu Aminu da Abokansa
Asali: Facebook

'Yan uwa da abokan arzikin Aliyu sun yi juyayi da alhinin rashinsa a dandalin sada zumunta.

DUBA WANNAN: 2019: Tsohon janar a rundunar soji ya shawarci masu takara da Buhari

YahayaAliyu Kakeyi, daya daga cikin wadanda suka nuna alhini da mutuwar Aliyu, ya rubuta a shafinsa na Facebook: "Inalillahi wainnailahi rajiun, ina mai bakin cikin sanar da ku mutuwar dan mu Aliyu Aminu (Abba), daya daga cikin jami'an tsaro 13 da mayakan kungiyar Boko Haram suka kashe a kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.

Ko a ranar Alhamis da ta gabata, sai da jaridar Legit.ng ta kawo maku labarin cewar wasu 'yan ta'adda da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kone makarantun firamare guda biyu da wani ginin sojoji a cikin kwanaki biyu a jihar Yobe.

An lalata makarantun biyu a wasu hare-hare da mayakan kungiyar suka kai a ranakun 24 da 26 ga watan Disamba a garuruwa Kuka-reta da Katarko, masu nisan kilomita 20 daga garin Damaturu, babban birnin jihar Yobe.

Mayakan sun kone makarantun firamaren Kuka-reta da Katarko da Ngaurawa da daruruwan 'yan gudun hijira ke halarta.

Lawani Babagana, dagachin garin Kuka-reta, ya ce makarantar firamaren garinsa na da mafi yawan dalibai a cikin ragowar makarantun da aka kone.

"Yanzu bamu da halin da yaran zasu shiga ba idan hutu ya kare," a cewar Babagana.

Alhaji Muhammad Goni, mazaunin garin Katarko, ya ce mayakan kungiyar Boko Haram sun taba kona makarantar garin a 2014 kafin gwamnatin ta kammala gyaranta a shekarar 205.

"Abun takaici ne ganin yadda 'yan Boko Haram suka sake kona makarantar garin Katarko. Babu abinda zamu iya yi a kan masu kawo harin don hatta sojoji da ya kamata su kare mu, gudu suke yo idan 'yan Boko Haram sun kawo hari. Dole muka gudu muka bar gidajen mu saboda sojoji ba zasu iya kare mu ba," a cewar sa.

Sai dai mazauna garin Damaturu sun nuna damuwa da yawaitar kai hare-hare kauyukan dake gefen garin, tare da yin zargin cewar mayakan na kungiyar na gwada karfinsu ne kafin su kawo hari babban birnin jihar na Yobe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel