'Kwararru ne suka kashe Alex Badeh inji na hannun damansa

'Kwararru ne suka kashe Alex Badeh inji na hannun damansa

Na hannun dama da kuma abokanan hulda ga tsohon shugaban hafsin dakarun sojin Najeriya, Marigayi Air Vice Marshal Alex Badeh, sun yi karin haske dangane da nau'in mutanen da ke da hannu na kisan sa da ya auku makonni kadan da suka gabata.

Mun samu cewa, wasu daga cikin na hannun dama da kuma abokanan hulda ga tsohon shugaban dakarun soji na Najeriya, Marigayi Air Vice Marshal Alex Badeh, sun bayyana cewa, kwararru da suka san hannun su ke da alhakin kashe tsohon sojan.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, 'yan bindiga sun harbe tsohon sojan yayin da yake kan hanyar sa ta dawowa daga gona a kauyen Gitata na jihar Nasarawa a ranar 18 ga watan Dasumba da ta gabata.

Tuni dai hukumar 'yan sanda reshen jihar Nasarawa, ta cikwikwiye wasu mutane biyar da ake zargin hannun sa cikin wannan muguwar ta'adda ta fasadi a ban kasa.

'Kwararru ne suka kashe Alex Badeh inji na hannun damansa

'Kwararru ne suka kashe Alex Badeh inji na hannun damansa
Source: Twitter

Daya daga cikin ababen zargin, Shu'aibu Rabo, ya yi ikirarin cewa sun harbe marigayi Badeh yayin da yunkurin hana su yi masa fashi da makami na wata dukiya mai tarin yawa da ya ke dauke da ita domin sayen wata gona bayan sun samu labarin hakan.

Sai dai 'yan uwa ga marigayi tsohon sojan sun karyata wannan ikirari da cewa kagaggen zance ne da hukumar 'yan sanda ta kitsa domin cimma wata boyayyar manufa.

Yayin ganawa da manema labarai na jaridar The Punch, daya daga cikin na hannun daman Marigayi badeh da ya bukaci a sakaya sunan sa ya bayyana cewa, hotunan da suka bayyana bayan aukuwar ta'addanci sun tabbatar da cewa wannan lamari ya sha gaban gama garin 'yan ta'adda.

Ya ke cewa, akwai lauje cikin nadi domin kuwa dukkanin alamu sun tabbatar da cewa an kitsa kisan marigayi Badeh tun ba yanzu ba kuma ko shakka ba bu kwararru ke da alhakin zartar da ta'addancin.

KARANTA KUMA: Buhari bai cancanci baƙin cikin rasuwar Marigayi Shagari ba bayan yiwa gwamnatin sa juyin mulki - Junaid

A nasa kaulin, wani daga abokanan Marigayi Badeh ya bayyana cewa, tsohon sojan ya yi gamo ne da azal a yayin da yake daf da shirin afkawa cikin kungiyar yakin nemzna zaben kujerar shugaban kasa ta jam'iyyar PDP domin goyon bayan dan takarar ta, Atiku Abubakar.

Kazalika wani na hannun daman marigayi ya bayyana cewa, mai aukuwar ta auku ne domin toshe bakin Marigayi Badeh wajen zayyana sunayen wadanda suka yi bushasha tare wajen cinye makudan kudaden al'ummar kasa da ake zargin sa da yashewa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel