Karin bayanin soji kan harin Boko Haram na jiya a garin Baga

Karin bayanin soji kan harin Boko Haram na jiya a garin Baga

- Soji sunce tabbas an kai hari a kansu a garin na Baga

- Sunce bayan sun dakile shirin na Boko Haram, kuma suna bin su har cikin dazukan da suke

- Ana sake samun hare-hare na Boko Haram a garin na Baga da kewaye

Karin bayanin soji kan harin Boko Haram na jiya a garin Baga

Karin bayanin soji kan harin Boko Haram na jiya a garin Baga
Source: UGC

Janar Sani Kukasheka, kakakin hukumar soji ta Najeriya, ya fidda sanarwa a shafinsu na Facebook, inda yake karin bayani ga manema labarai da ma 'yan Najeriya kan harin da Boko Haram suka kai a jiya a Baga, kan bataliyar soji.

A cewar sanarwar, tabbas Boko Haram sun kai hari kan bataliyar soji ta bakwai, watau 7 Brigade, wadda ke aiki da hadakar sojojin kasashen yankin, don karasa kakkabe mayakan IS da Boko Haram.

Ya kara da cewa, bayan da soji suka dakile shirin, sun kuma kai raraka inda maboyar mayakan take a yankin da kewaye, duk a jiya Laraba zuwa yau Alhamis, kuma suna samun nasara.

DUBA WANNAN: An sake kai hari a ofishin kamfe na APC a kudu, an kona musu motoci

Harin dai da suka fara kawowa soji tun karfe bakwai, sai da aka shafe duk daren ana ba-takashi da Boko Haram din a kokarin su na sai sun sha kan soji sun kwaci yankin da ma satar makamai, kamar yadda suka yi a Metele a watan jiya.

Sai da aka karo dakarun sojin ruwa da na Lafiya dole, suka agazawa sojin don daqile mummunan shirin na Boko Haram, an kuwa yi nasara.

An kuma karo soji da zasu bi kadin ceton ko an saci wasu daga jama'a ko soji, ko ma gawarwakin da aka baras na mayakan, a fadan na jiya zuwa safiyar yau, sanarwar ta fadi.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel