Wani Mutumi ya kashe Uwar yaran sa a kan kudin magani N1500 a Jihar Neja

Wani Mutumi ya kashe Uwar yaran sa a kan kudin magani N1500 a Jihar Neja

Mun samu wani labari mai ban takaici cewa wani Bawan Allah mai suna Malam Jafaru Bawa da ke cikin Garin Sabon Garin Bobi a karamar hukumar Mariga a Jihar Neja yayi wa Matar sa mugun duka har ta kai ga mutuwa.

Wani Mutumi ya kashe Uwar yaran sa a kan kudin magani N1500 a Jihar Neja

Mahafiyar marigayiyar ta bayyana cewa surukin ta ya kashe diyar su da duka
Source: Depositphotos

Wannan mutumi da ke zaune a cikin Jihar Neja ya kashe matar sa mai suna Amina Jafaru ne a kan abin da bai kai ya kawo ba. Kamar yadda mu ka samu labari, rikici ya barke tsakanin ma’auratan ne saboda rashin lafiyar ‘Ya ‘yan su.

Kamar yadda wani wanda ya san abin da ya faru ya bayyanawa jaridar Daily Trust a Garin Sabon Garin Bobi, rikici ya kaure ne a kan biyan kudin maganin daya daga cikin ‘Ya ‘yan wannan ma’aurata wanda yake fama da cuta a asibiti.

KU KARANTA: 'Yan sandan Najeriya sun karyata cewa jami'anta sun tsere a Borno

Takaddamar da ta shiga tsakanin Jafaru da Mai dakin sa Amina ta kai har Mijin ya dirka mata duka. Wannan ya sa dole makwabta su ka nemi su kawo agaji, bayan an ceci wannan Baiwar Allah, sai aka maida ta wajen iyayen ta a gida.

Bayan an tsere da Marigayiyar zuwa gidan Iyayen ta ne sai hawan jini ya kamata ta, dole ta sa aka ruga da ita zuwa wani asibiti. Ko da aka je asibiti dai sai aka iske ta cika. Ba mamaki dai yanzu Jami’an ‘Yan Sanda su fara binciken lamarin.

Jafar Bawa yayi wa Malama Amina ‘dan karen duka ne bayan da aka kwantar da wani yaron su a asibiti, inda ya nemi ta biya rabin kudin magani har N1500. Marigayiyar ta sha ‘dan banzan kashi ne bayan ta fadawa Mai gidan ta ba ta da kudi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel