Faifan bidiyo: Jiki magayi, sai mun ja Buhari - Matasan Zamfara

Faifan bidiyo: Jiki magayi, sai mun ja Buhari - Matasan Zamfara

- A yau, Litinin, ne gungun matasa suka yi zanga-zangar nuna fushinsu da kashe-kashen dake faruwa a jihar Zamfara.

- Yayin zanga-zangar, gungun matasa sun rera waka da rawar "jiki magayi, sai mun canja Buhari"

- Wasu rahotanni sun ce jami'an 'yan sanda sun yi harbi domin tarwatsa masu zanga-zangar

Hukumar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Zamfara ta bayar a sanarwar takaita zirga-zirga a karamara hukumar Tsafe da ke jihar sakamakon zanga-zangar nuna damuwa kan yawaitar kashe-kashe a jihar wadda daga bisani ya haifar da rudani da kone-kone.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa wasu matasa sun fito suna zanga-zangar nuna damuwar su kan lamarin rashin tsaro a jihar inda aka ce sun rufe tittin da ya sada Funtua, Zaria, Sokoto, Kebbi da Kaduna.

Rahotanni sun ce matasan sun kona sakatariyar karamar hukumar Tsafe kuma sun nufi gidan shugaban karamar hukumar.

Matasan sun rera wakar, "jiki magayi, sai mun canja Buhari", kamar yadda zaku iya gani a cikin wannan faifan bidiyon:

Jami'n hulda da jama'a na 'yan sandan jihar, Mohammad Shehu ya sanar da cewar an al'umma za su iya fitowa suyi harkokinsu ne daga karfe 7 na safe zuwa karfe 6 na yamma kamar yadda TheCable ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Albashin Dariye: SERAP ta maka Saraki a kotu

Ya ce dokar takaita zirga-zirgar za ta cigaba da aiki har sai nan gaba idan abubuwan sun lafa a garin. 'Yan ta'adda sun kai hari a kauyen Magami da ke karamar hukumar Maradun a ranar Asabar inda suka kashe mutane da dama.

Tuni dai hukumar 'yan sandan ta bayar da umurnin aikewa da karin 'yan sanda zuwa jihar na Zamfara domin su taimaka wajen bin sahun 'yan ta'addan tare da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel