Dalla-Dalla: Tsoho dan shekaru 85 da aka kama da zuciyar mutum ya yi bayani

Dalla-Dalla: Tsoho dan shekaru 85 da aka kama da zuciyar mutum ya yi bayani

An kama wani tsohon boka, Samuel Hunsu, mai shekaru 85, a garin Abeokuta, jihar Ogun da danyun zuciyoyin mutane.

Yayin bajakolin Hunsu ga manema labarai, jami'an 'yan sanda na ofishin shiyya ta 2 dake Onikan a jihar Legas, sun ce dattijon ya amince da amfani da sassan jikin mutane domin tsafin kudi.

Sai dai, Hunsu ya ce wani mutum ne mai suna Abiodun ya kawo masa zuciyar domin a yi masa tsafin samun kudi.

A cewar dattijo Hunsu, "Abiodun ne ya kawo min zuciyar bayan ya tuntube ni domin hada masa tsafin kudi kuma na fada masa abubuwan ake bukata. Nima nayi mamakin ganinsa da zuciyar mutum. Sai da na tambaye shi inda ya samo zuciyar mutum, amma sai yace ya ciro ta ne a jikin wani barawo da aka kashe a jihar Ogun. Bayan ya tafi ne sai na adana zuciyar cikin wasu sinadarai don kar ta lalace, har zuwa lokacin da zai dawo. Ban san Abiodun ba kuma ban san inda yake da zama ba. Ni dai kawai ya ce min ya zo wurina ne tun daga jihar Kwara."

Sai dai jami'an 'yan sanda ta ce sun samu rahoton cewar mutane biyu sun mutu a sansanin matsafin.

Dalla-Dalla: Tsoho dan shekaru 85 da aka kama da zuciyar mutum ya yi bayani
Samuel Hunsu
Asali: Facebook

A cewar 'yan sanda: "da muka tambaye shi a kan mutanen da suka mutu a sansaninsa na tsafi, sai ya ce sun mutu ne yayin zaman jinya kuma ya binne su ba tare da mayar da su ga iyalinsu ba. Bayan mun samo izinin bincike daga kotu ne muka gano zuciyoyin mutane a cikin wata roba kuma bincike ya nuna mana cewar zuciyoyin sun samu tsawon sati biyu a ajiye cikin robar."

DUBA WANNAN: Hoton kwamandan Boko Haram da Abba Kyari ya kama a Legas

Lawal Shehu, mataimakin babban sifeton rundunar 'yan sanda mai kula da shiyya ta 2, ya ce a ranar 17 ga watan Disamba ne suka samu rahoton cewar wani matsafi Samuel Hunsu na dauke da sassan jikin mutane.

Sannan ya kara da cewa, "ba tare da bata lokaci ba muka tura jami'an 'yan sanda zuwa sansanin matsafin inda suka same shi da zuciyar da mutum a sansaninsa dake kauyen Ireke a jihar Ogun. Yayin da muke gudanar da bincike ne ya shaida mana cewar an samu zuciyar ne daga jikin wani barawo da aka kashe yankin Ijoko dake jihar Ogun kuma ya fada mana cewar wani ne mai suna Abbey ya cire zuciyar daga jikin barawon."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel