Tsakanin Atiku da Buhari: Kungiyar Afenifere ta 'yan kabilar Yoruba ta zabi nata

Tsakanin Atiku da Buhari: Kungiyar Afenifere ta 'yan kabilar Yoruba ta zabi nata

Bayan daukan lokaci tana tuntuba da mahawara, babbar kungiyar 'yan kabilar Yoruba ta kasa, Afenifere, ta zabi shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin dan takarar da zata goyawa baya a zaben shekarar 2019.

Kungiyar ta nesanta kanta da tsagin shugabancin Ayo Adebanjo da ya bayyana goyon baya ga takarar Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP.

Afenifere ta bayyana hakan ne yayin taron ta na masu ruwa da tsaki da tayi Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Taron ya samu halartar wakilan kungiyar daga dukkan jihohin yankin kudu maso yamma guda 6.

Da yake magana da manema labarai bayan kammala taron kungiyar na sirri, Cif Biodun Akinfase, kakakin Afenifere, ya bayyana tsagin da Cif Ayo Adebanjo, ke jagoranta da 'yan hana ruwa gudu tare da nesanta kansu daga harkokin tsagin kungiyar.

Tsakanin Atiku da Buhari: Kungiyar Afenifere ta 'yan kabilar Yoruba ta zabi nata

Shugaban kungiyar Afenifer
Source: Facebook

Kazalika ya bayyana cewar 'yan kabilar Yoruba zasu yi wani gagarumin taro a ranar 29 ga watan Janairu domin nuna goyon baya ga Buhari da Buhari.

"Muna masu sanar da duniya cewar kungiyar Afenifere daya ce tun lokacin Awolowo kuma tana goyon bayan takarar Buhari da Osinbajo ne a zaben shekarar 2019.

DUBA WANNAN: Abinda Buhari ya kamata ya yi bayan 'yan majalisa sun yi masa ihu - Atiku

"Wani tsagin kungiyar Afenifere karkashin jagorancin Cif Ayo Adebanjo dake goyon bayan takarar Atiku, ba tare yake da mu ba. Kabilar Yoruba a dinke ta take tun lokacin Awolowo duk da ana samun dan sabani tsakanin mabiya. Kungiyar Afenifere ta gaskiya ita ce wacce dattijo Ayo Fasanmi ke jagoranta kuma tana da jam'iyyar APC a duk jihohin kabilar Yoruba guda 6," a cewar sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel