2019: Atiku zai yi nasara idan har babu magudi - Babangida Aliyu

2019: Atiku zai yi nasara idan har babu magudi - Babangida Aliyu

Babangida Aliyu, tsohon gwamnan jihar Neja, ya ce dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ne zai lashe zaben shekarar 2019 idan babu magudi.

Aliyu ya fadi haka ne yayin tattaunawa da manema labarai a garin Kaduna, a yau, Lahadi.

Ya bukaci hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da hukumomi tsaro su yi aikinsu ba tare da nuna goyon bayan wani bangare ba.

"Ina son ku yarda da ni cewar a jiha ta, idan za a yi zabe na gaskiya, ba tare da magudi ba, idan ba za ai amfani da jami'an tsaro ba, zamu ci zabe, Atiku zai kayar da Buhari," a cewar tsohon gwamnan.

A wani labarin mai kamanceceniya da wannan da legit.ng ta kawo maku, kun ji cewar jam'iyyar APC ta kara jaddada aniyarta kan cewar shugaba Buhari zai mika mulki ga dan kabilar Igbo bayan gama wa'adinsa a shekarar 2023, a cewar sakataren gwamnatin tarayya, Boss Gida Mustapha.

2019: Atiku zai yi nasara idan har babu magudi - Babangida Aliyu
Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Sai dai wannan mataki na Mustapha ya saba da na ministan aiyuka, gidajen, da lantarki, Babatunde Raji Fashola, na cewar shugaba Buhari zai mika mulki ga dan kabilar Yoruba a 2023.

Da yake magana yayin jawabi ga kwamitin masu goyon bayan Buhari a Umuahia, jihar Abiya, a karshen makon na, Mustapha ya bayar da tabbacin cewar shugaba Buhari ga dan kabilar Igbo idan ya kammala wa'adinsa.

DUBA WANNAN: An kashe mutane 4 a wurin kaddamar da kamfen din Ganduje a Kano

A cewar sa, hanya mafi sauki da 'yan kabilar zasu samu damar yin mulkin Najeriya shine su goyawa Buhari a zabukan shekarar 2019.

Mustapha, da yake magana ta bakin wakilinsa, Mista Gideon Sammani, ya ce ya yi farinciki da karbuwar da jam'iyyar APC ke kara samu a yankin kudu maso gabas na 'yan kabilar Igbo. Ya kara da cewar daga abinda ya gani yana da yakinin cewar shugaba Buhari zai lashe zabe a yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel