Gagararrun 'yan fashi sun fada komar 'yan sanda a Katsina, hotuna

Gagararrun 'yan fashi sun fada komar 'yan sanda a Katsina, hotuna

Rundunar 'yan sandan Najeriya, reshen jihar Katsina, ta sanar da samun nasarar damke wata tawagar 'yan fashi da makami ta mutane biyar da suka dade suna addabar garuruwan Jihar Katsina da kewaye.

Jam'ian rundunar 'yan sandan sun yi nasarar cafke 'yan fashin ne a jiya, Juma'a, bayan aikata wani fashi a garin Funtuwa.

Isa Gambo, kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Katsina, ya bayyana cewar alhaki ne ya kama 'yan fashin bayan sun aikata fashi a gidan wani mutum mai suna Haruna Idris dake unguwar Dan-Dutse a garin Funtuwa.

Gambo ya lissafa sunayen 'yan fashin kamar haka: Umar Yahaya (shekaru 24), Abdulmalik Yahaya (shekaru 20), Abdulrashid Musa (shekaru 20), Abdurrahaman Suleiman da (shekaru 21), dukkansu mazauna kauyen Maigamji dake karkashin karamar hukumar Funtuwa.

Gagararrun 'yan fashi sun fada komar 'yan sanda a Katsina, hotuna
Gagararrun 'yan fashi sun fada komar 'yan sanda a Katsina
Asali: Facebook

Ya kara da cewar an yi nasarar samun makamai da suka hada da bindiga, bindigar wasan yara daya, wukake masu kaifi guda biyu, adda, cocilan, dubu tara da naira tamanin, da wayoyin hannu 4, da kuma hular soji guda daya.

Kazalika rundunar 'yan sandan ta sanar da kama mutane 12 da ake zargi da satar mutane da satar shanu a garuruwan Dandume da Safana.

An kama su ne yayin da suka kai farmaki kauyen Dallawa Mahuta inda suka kashe wani matashi mai suna Aminu Maharazu, mai shekaru 20.

DUBA WANNAN: Faduwa jarrabawa: Hameed Ali zai yi kora a hukumar kwastam

Sun shiga hannu ne bayan artabu da jami'an 'yan sanda. Mutanen kauyen sun kashe uku daga cikin 'yan fashin kafin karasowar jami'an 'yan sanda, ragowar kuma sun guda zuwa cikin daji.

An baza jam'ian 'yan sanda zuwa cikin jejin domin kama ragowar da suka gudu.

An gano gawar Isiya Bello, dan asalin karamar hukumar Sabuwa, kasurgumin mai garkuwa da mutane da ya addabi garuruwan Dandume, Sabuwa, da Ankara, daga cikin 'yan ta'addar da mutanen kauyen suka kashe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel