Jam'iyyar SDP ta dauki Gabam, madadin dan takarar mataimakin kujerar shugaban kasa

Jam'iyyar SDP ta dauki Gabam, madadin dan takarar mataimakin kujerar shugaban kasa

- Jam'iyyar SDP ta sauya dan takarar mataimakin kujerar shugaban kasa

- Dakta Junaidu Muhammad, ya janye takararsa ta kujerar mataimakin shugaban kasa na a jam'iyyar SDP

- Jam'iyyar SDP ta zabi Mista Shehu Musa Gabam a matsayin sabon dan takarar ta na kujerar mataimakin shugaban kasa a zaben 2019

Mun samu rahoton cewa, jam'iyyar SDP Social Democratic Party, ta sauya abokin takarar kujerar shugaban kasa na zaben 2019, Dakta Muhammad Junaidu, inda ta dauko Mista Shehu Musa Gabam, wanda ya kasance sakataren jam'iyyar na kasa.

Sakataren hulda da al'umma na jam'iyyar, Alfa Muhammad, shine ya bayar da shaidar hakan a jiya Alhamis cikin babban birnin kasar nan na tarayya kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito.

Yake cewa, tuni jam'iyyar ta rigaya da sauya madadin Junaidu, inda ta zabi Gabam a matsayin dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar, biyo bayan shawarwari da tuntube-tuntube na jiga-jigan jam'iyyar.

Donald Duke; dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar SDP
Donald Duke; dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar SDP
Asali: Depositphotos

Hukuncin jam'iyyar na sauya abokin tafiya na da takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar, Donald Duke, ya bayu ne a bisa dalilai na tsare-tsare gami da tumke damarar fafatawa a yayin babban zaben kasa na 2019.

Mista Alfa ya ci gaba da cewa, kasancewar Junaidu dan jam'iyya na gani kashe ni, ya sanya yayi na'am da wannan lamari na sauya madadinsa a matsayin dan takarar kujerar mataimakin shugaban kasa sakamakon kishi na ci gaban da cimma nasarar jam'iyyar da ta mamaye zuciyar sa.

KARANTA KUMA: Yarinya 'Yar shekara 7 ta yi karar Mahaifin ta a Kasar Indiya

A sanadiyar haka Dakta Junaidu ya janye takararsa tare da rattabu kan takardun na yarjewa da amincewarsa bisa tanadi na dokokin hukumar zabe ta kasa watau INEC.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC, ta kwace wani katafaren gida mai daraja ta Naira miliyan 500 mallakin tsohon gwamnan jihar Adamawa, Umar Fintiri.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel