Gobara da sanyin safiya ta kone wani gida a jihar Kano

Gobara da sanyin safiya ta kone wani gida a jihar Kano

Za ku ji cewa, wata wutar gobara da ta auku da sanyin safiyar yau ta Alhamis, ta yi babbar ta'asa yayin da ta salwantar dukiya daidai gwargwado a cikin babban birni na Kanon Dabo da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Hukumar kwana-kwana ta jihar Kano, ta bayyana cewa da sanyin safiyar yau ta Alhamis, wutar gobara ta kone wani babban gida kurmus a Unguwar Hotoro da ke tantagwaryar birnin Kano.

Kakakin hukumar, Alhaji Sa'idu Muhammad, shine ya bayar da shaidar hakan yayin ganawar sa da manema labarai. Ya ke cewa gobarar ta auku ne da misalin karfe 2.52 na safiyar yau ta Alhamis 13 ga watan Dasumba.

Gobara da sanyin safiya ta kone wani gida a jihar Kano
Gobara da sanyin safiya ta kone wani gida a jihar Kano
Asali: Depositphotos

Alhaji Sa'idu ya bayyana cewa, tsautsayin da ya auku a babban gidan ya lashe dukiya mai tarin yawa da kawowa yanzu bincike ya gaza tabbatar da sanadin aukuwar wannan mummunar gobara.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, Alhaji Sa'idu ya gargadi al'umma dangane da bayar da kulawa mai girman gaske yayin amfani da ababe ma su haddasa gobara musamman a wannan lokaci na hunturu da annobar gobara ta fi aukuwa.

KARANTA KUMA: Saraki zai halarci bikin kaddamar da tsare-tsaren ci gaban Afirka a kasar Amurka

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, hukumar kwana-kwana ta jihar Kano, ta kuma bayar da sanarwar cewa wani Matashi, Halifa Mamuda, ya riga mu gidan gaskiya yayin da ya nutse cikin wani tafki dake Unguwar Dan Agundi a safiyar yau Alhamis.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Ministan Makamashi Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba bu yadda ta iya da karanci da kuma rashin wutar lantarki a Najeriya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng