2019: Buhari ya fadi sakayyar da zai yiwa 'yan Najeriya idan suka sake zaben shi

2019: Buhari ya fadi sakayyar da zai yiwa 'yan Najeriya idan suka sake zaben shi

A yayin da yakin neman zabe ke kara daukan zafi, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar zai sakawa masoya da masu goyon bayansa da manyan alherai bisa amincewa da shi da suka nuna.

Shugaba Buhari ya bayar da wannan tabbaci ne a jiya, Laraba, yayin kaddamar da wata kungiyar magoya bayansa a Abuja.

Yayin jawabinsa a wurin taron taron, shugaba Buhari ya nuna jin dadinsa tare da yiwa kungiyar magoya bayan nasa godiya, yana mai cewa, "wasu mutane da kungiyoyi sun yi fushi da mu saboda bamu iya biyan bukatunsu ba."

2019: Buhari ya fadi sakayyar da zai yiwa 'yan Najeriya idan suka sake zaben shi
2019: Buhari ya fadi sakayyar da zai yiwa 'yan Najeriya idan suka sake zaben shi
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Atiku ya fadawa CAN nufinsa ga Najeriya

"Ina mai tabbatar maku wannan karon wahalar masoya da masu goyon bayan mu ba zata fadi kasa a banza ba," a kalaman Buhari.

Sannan ya cigaba da cewa, "ganin halacci daga masoya irinku kan bani karfin gwuiwa koda yaushe."

A nata bangaren, kungiyar ta yiwa shugaba Buhari alkawarin inganta aiyukanta domin ganin ya sake lashe zaben shekarar 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng