Rashin kudin shiga ya sa Najeriya na neman yi wa Kungiyar OPEC gardama

Rashin kudin shiga ya sa Najeriya na neman yi wa Kungiyar OPEC gardama

- Tattalin arzikin Najeriya bai motsa yadda aka sa rai a karshen shekarar 2018 ba

- Wannan ya sa ake tunani Najeriya ba za ta rage adadin man da ta ke hakowa ba

- Gwamnati ba ta samu kudin da ta kiyasta a kasafin kudin wannan shekarar ba

Rashin kudin shiga ya sa Najeriya na neman yi wa Kungiyar OPEC gardama
Ministan man fetur na Najeriya Dr. Emmanuel Ibe Kachikwu
Asali: Depositphotos

Kwanan nan ne Hukumar NBS mai tara alkaluman Najeriya ta fitar da rahoton yadda tattalin arzikin Kasar Najeriya ya kaya a karshen shekarar nan. Har yanzu abubuwa dai ba su mikewa kamar yadda ake sa rai ba.

Tattalin arzikin Najeriya ya motsa da 1.8% a cikin watanni 3 da su ka wuce na shekarar bana. Sai dai duk da haka Jaridar Bloomberg ta Kasar waje ta bayyana cewa Gwamnati na fama da karancin kudi a halin yanzu a Kasar.

KU KARANTA: Qatar za ta fice ta bar Najeriya da sauran Kasashe a Kungiyar OPEC

A cikin Watan Oktoba, Najeriya ta samu kusan Dala Biliayan 2 watau kimanin Naira Biliyan 700 daga man fetur, wannan kudi dai da kadan ya haura rabin abin da ake tsammani za a samu a kasafin kudin wannan shekarar.

Wannan ne ya sa ake tunani Najeriya za tayi wa Kungiyar OPEC gardama bayan an yi yarjejeniyar rage adadin man fetur da ake hakowa a kowace rana. Wannan mataki da OPEC za ta dauka zai kawowa Najeriya cikas.

Karamin Ministan fetur na kasar, Ibe Kachikwu ya nuna cewa Najeriya na bukatar kudin shiga. A kowane wata dai kasar tana samun kasa da abin da tayi kasafin samu a farkon shekara don haka ake kokarin zage dantse kafin 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel