Lokaci ya yi da Atiku zai zama shugaban kasar Najeriya - Ortom

Lokaci ya yi da Atiku zai zama shugaban kasar Najeriya - Ortom

A ranar Larabar da ta gabace mu, gwamnan jihar Benuwe Samuel Ortom, ya bayyana cewa lokaci ya karato da dan takarar kejerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, zai zamto shugaban kasar Najeriya.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, gwamna Ortom ya bayyana hakan ne yayin karbar bakuncin kungiyar Matan yankin Arewa ta Tsakiya magoya bayan Atiku, da ta ziyarce shi har fada bisa jagorancin shugaba ta kungiyar, Ms Dorcas Din.

Gwamna Ortom ya bayyana cewa, a halin yanzu tafiya ta kan kama ta cimma nasarar Atiku yayin babban zaben kasa na badi.

Lokaci ya yi da Atiku zai zama shugaban kasar Najeriya - Ortom
Lokaci ya yi da Atiku zai zama shugaban kasar Najeriya - Ortom
Asali: Depositphotos

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamna Ortom ya kyautata zaton sa gami da fata na gari dangane da yadda jagorancin tsohon mataimakin shugaban kasar nan zai fidda Najeriya zuwa ga tudun tsira tare da habaka tattalin arziki ta kowace fuska.

Gwamna Ortom ya kuma bayyana takaicin sa dangane da yadda gwamnati mai ci ta APC ke ribatar karfin ikon ta wajen muzgunawa mambobin jam'iyyar adawa ta hanyar yi ma su cunen hukumomi ma su hana yiwa tattalin arziki zagon kasa.

Ya sake jaddada matsayarsa tare da bayar da tabbacinsa kan nasarar Atiku a babban zaben kasa na 2019.

KARANTA KUMA: Ba bu ruwan Gwamnatin Tarayya da rashin wutar lantarki a Najeriya - Fashola

A na ta bangaren, jagorar kungiyar Ms Din, ta yi korafi dangane da yadda gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta gaza sanya Mata cikin tafiyar ta tsawon shekaru uku da ta shafe a bisa kujerar mulki.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ta daura damarar da kudirtar aniyya ta aurar da zaurawa 3000 a babban birni na Kanon Dabo.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng