Tsawa ta hallaka Mutane 10 a Kasar Mozambique

Tsawa ta hallaka Mutane 10 a Kasar Mozambique

Tsautsayi da ba ya wuci ranarsa kuma amsa kiran ajali ba bu makawa mun samu cewa, akalla rayukan Mutane 10 sun salwanta yayin da tsawo da fada kansu a yankunan Tsakiya da kuma Arewacin kasar Mozambique dake nahiyyar Afirka.

Kamar yadda shafin jaridar BBC Hausa ya ruwaito, wannan lamari ya auku ne a sanadiyar mamakon ruwan sama mai hadi da tsawo gami da iska mai karfin gaske da kwaranya a kasar da ke Kudancin Afirka.

Yawaitar mace-macen kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito sun auku ne a karshen makon da ya gabace mu, musamman a yankunan Sofala, Zambezia, Niassa da kuma yankin Manica da tete.

Aukuwar wannan annoba ta salwantar da muhallan kimanin iyalai 500 da ambaliyar ruwa ta yi awon gaba da gidaje da kuma dukiyarsu.

Tsawa ta hallaka Mutane 10 a Kasar Mozambique
Tsawa ta hallaka Mutane 10 a Kasar Mozambique
Asali: Depositphotos

Shugabar cibiyar bayar da agajin gaggawa ta kasar Mozambique, Agusta Maita, ta shawarci al'umma kan daukar matakai na riga kafi domin tseratar da rayukan su da cewa, ba bu wani hanzari ga ma su fitowa yayin da ruwan sama mai tsanani ke kwaranya.

Rahotanni sun bayyana cewa, tarihi ya tabbatar da yadda kasar Mozambique ta fuskanci annobar ambaliyar ruwan sama mafi muni a shekarar 2000, inda rayukan kimanin Mutane 700 suka salwanta yayin da fiye da miliyan daya suka rasa muhallansu.

KARANTA KUMA: Gwamna El-rufa'i zai dauki Malaman Makaranta 7000 a jihar Kaduna

Binciken masana kimiyya da kuma sauyin yanayi ya tabbatar da cewa, lokaci na damina na farawa a watan Oktoba zuwa watan Maris cikin kowace shekara a Kasar ta Mozambique.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, binciken manema labarai na Al-Jazeera ya tabbatar da yadda ambaliyar ruwan sama ta yi sanadiyar salwantar rayukan Mutane 100 cikin jihohi 10 a Kasar Najeriya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng