Nasarorin Buhari ya fi na shekaru 16 da PDP ta yi tana mulki – Omo-Agege
- Sanata Ovie Omo-Agege ya bayyana shekaru uku da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi yana mulki a masayin mai cike da nasara idan aka kwatanta da shekaru 16 da jam’iyyar PDP tayi
- Dan majalisan ya bayyana hakan ne a Ughelli, jihar Delta lokacin kaddamar da kungiyar kamfen dinsa na mutum 400 karkashin jagorancin Cif Francis Atanoneyovwin.
- Yace gwamnat ta yi matukar kokari wajen yakar cin hani da rashawa, da kuma yaki da ta’addanci a yankin arewa maso gabashin kasar kuma suna kan nasara a yakin
Sanata mai wakiltan yankin Delta ta tsakiya a majalisar dokokin kasar, Sanata Ovie Omo-Agege ya bayyana shekaru uku da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi yana mulki a masayin mai cike da nasara ga yan Najeriya idan aka kwatanta da shekaru 16 da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tayi.
Dan majalisan ya bayyana hakan ne a Ughelli, jihar Delta lokacin kaddamar da kungiyar kamfen dinsa na mutum 400 karkashin jagorancin Cif Francis Atanoneyovwin.

Asali: Depositphotos
Omo-Agege yayinda yake yaba ma gwamnatin APC yayi bayanin cewa gwamnat ta yi matukar kokari wajen yakar cin hani da rashawa, da kuma yaki da ta’addanci a yankin arewa maso gabashin kasar kuma suna kan nasara a yakin.
KU KARANTA KUMA: 2019: Gwamnonin APC 3 sun yi ganawar sirri da Omisore
Yace: “Ta hanar shirin ci gaba da gwamnatin tayi na N-Power, TradersMoni da ciyar da yaran makaranta, yan Najeriya da dama sun samu aikin yi don haka sun cancanci a sake zabar gwamnatin APC domin ci gaban wannan shirin."
Ya kuma jadadda tarin kokarin da Buhari yayi a jihar Delta ta hanyar gina manyan hanyoyi fiye da na gwamnatocin jiha.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng