Yan ta’addan Boko Haram sun kai farmaki a Madagali
- Yan ta’addan Boko Haram sun kai hari a yankin Madagali da ke jihar Adamawa sannan inda suka yi kone-kone da harbe-harbe
- Sun kai farmaki ne ta yankin kauyen Yahza dake tsakanin jihohin biyu inda suka yi barna masu dinbin yawa, ciki harda gidaje da kuma amfanin gona
- Yanzu haka al’umman wadannan yankuna na cikin wani mawuyacin hali na zaman dar-dar da fargaba
Labari da ke zuwa mana ya nuna cewa wasu yan ta’addan Boko Haram sun kai hari a yankin Madagali da ke jihar Adamawa sannan kuma daura da dajin Sambisa inda suka yi kone-kone da harbe-harbe.
Kamar yadda al’umman yankin suka tabbatar, yan ta’addan sun kai farmaki ne ta yankin kauyen Yahza dake tsakanin jihohin biyu inda suka yi barna masu dinbin yawa, ciki harda gidaje da kuma amfanin gona.

Asali: Depositphotos
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sirrinta sunansa, yace yanzu haka al’umman wadannan yankuna na cikin wani mawuyacin hali na zaman dar-dar da fargaba.
KU KARANTA KUMA: Abun mamaki: Wasu abubuwa 5 dake lalata hunhu bayan sigari
Koda yake kawo yanzu hukumomin tsaro basu yi wani cikakken bayani ba akan al’amarin, amma kuma dan Majalisar Wakilai dake wakiltar yankin Madagali da Michika, Hon Adamu Kamale, ya tabbatar da wannan sabon harin ya kuma koka game da sabbin hare-haren da ake kaiwa yankunan, ya kuma nemi a kara yawan sojoji a garuruwan.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng