Dana yayi nadama – Mahaifin Abdulmutallab ya roki gwamnatin Amurka da ta yafe mai

Dana yayi nadama – Mahaifin Abdulmutallab ya roki gwamnatin Amurka da ta yafe mai

Mahaifin Umar Farouk Abdulmutallab, wanda aka kama da bam a shekarar 2009, ya bukaci gwamnatin Najeriya da gwamnatin Amurka da su yafe ma dansa akan tuhumar ta’addancin da ake yi masa.

Umar Abdulmutallab, mahaifin Umar Farouk Abdulmutallab, wanda aka fi sani da 'Underwear Bomber', ya bukaci gwamnatin Najeriya da gwamnatin Amurka da su yafe ma dansa akan tuhumar ta’addancin 2009.

An tsare Abdulmutallab, wanda ke da shekaru 23 a lokacin da aka kama shi, akan yunkurin tayar da bam wanda ya boye a karkashin rigansa yayinda yake cikin jirgin sama, wanda ya tashi daga Amsterdam zuwa Detroit, Michigan, a ranar Kirismetin 2009.

A ranar 16 ga watan Fabrairun 2012, an yanke masa hukuncin daurin raio-da-rai da shekaru 50 a killace a kasar Amurka.

Dana yayi nadama – Mahaifin Abdulmutallab ya roki gwamnatin Amurka da ta yafe mai
Dana yayi nadama – Mahaifin Abdulmutallab ya roki gwamnatin Amurka da ta yafe mai
Asali: UGC

Kusan shekaru tara bayan kamun nashi, mahaifinsa na kira ga gwamnati da ta yafe ma dansa.

Daily Trust ta ruwaito cewa mahaifin Abdulmutallab wanda ya samu wakilcin babban shugaban gidauniyar Jaiz, Imam Shuaib Abdullahi ya yi rokon a wani taro inda kungiyar kare hakki ta HURMA ta karrama shi a matsayin majidadin mutane a Lagas.

Abdullahi wanda yayi Magana a madadinsa yace: “A duk lokacin da na tattauna dashi, sai yace mun Imam, ‘Na yi nawa a matsayina na dan Najeriya, nayi nasarar ceto rayukan mutane sama da 270 saboda da ace bam dinnan ya tashi, buna maganan rayuka 279 ne za su salwanta. Ya ce burin shi ya cika tunda ya ceci rayukan mutane.

KU KARANTA KUMA: Kada ku zabi yan siyasar a mutu ko ayi rai – Shugaban CAN

“Hakazalika yana matukar yi masa ciwo ace dan mutum na daure, inda aka yi mashi hukuncin daurin rai-da-rai har sau uku. Yace bai sani ba idan zai yiwu ya sake ganin dansa yana raye amma idan nufin Allah kenan cewa ba za’a saki dansa ba sannan ya mutu, hakan ce zata kasance.

“Amma a kasar zuciyarsa, yana son wani lamari ta yadda za’a sake duba abun musamman a yanzu da dan nasa yayi nadama sosai saboda kusan shekaru 12 kenan zai je, dan nasa na kebe inda baya mu’amala da bil adama har ta kai idan za’a bashi abinci, ana bashi ne ta tsarin kai tsaye.

“Ga dan da ba zai iya fadin ko wani yanayi ake ba imam safe, rana ko dare ne, wani halin bakin ciki kuke ganin mahaifinsa zai kasance a ciki.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng