Yanzu Yanzu: EFCC ta tsare Doyin Okupe
- Hukumar EFCC ta tsare mai ba da shawara ga Darakta Janar na kungiyar kamfen din dan takarar shugaban kasa na PDP akan labarai, Doyin Okupe
- Kakakin jam’iyyar PDP Kola Ologbodiyan ya bayyana hakan a shafin twitter
- Ya ce yanzu lokaci ne na tozarci, cin zarafi da barazana ga mambobin jam’iyyar PDP
Hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ta tsare hadimin Darakta Janar na kungiyar kamfen din dan takarar shugaban kasa na PDP, Doyin Okupe.
Kakakin jam’iyyar PDP Kola Ologbodiyan ya bayyana cewa yanzu a shiga lokacin ci wa mambobin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) mutunci da tozarci tare da barazana.

Asali: Depositphotos
Kola Ologbondiyan ya wallafa a shafin twitter a daren ranar Litinin, 10 ga watan Disamba cewa: “Hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta kama hadimin Darakta Janar na kungiyar kamfen din shugaban kasa na PDP, @doyinokupe.
“Yanzu lokaci ne na tozarci, cin zarafi da barazana ga mambobin jam’iyyar PDP”, cewar shi.
KU KARANTA KUMA: Boko Haram na iko da kananan hukumomi 17 a Borno - Sani Zoro
A baya mun ji cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa sun kai mamaya gidan da ýaýan Atiku Abubakar biyu ke zama a Abuja a karshen mako, jaridar Premium Times ta ruwaito.
Haka zalika Chimeka Orji, dan tsohon gwamnan jihar Abia, Theodore Orji na zama ne a gidan. An kuma rahoto cewa jami’an hukumar yaki da rashawan sun binciki sashinsa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng