Yaki da shan kwayoyi: Buhari ya kafa kwamiti guda biyu
Bisa la'akari da yadda matsalar shan miyagun kwayoyi ke kara zama ruwan dare, a yau, Litinin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa kwamiti guda biyu da zasu fitar da hanyoyin da za a magance matsalar tu'ammali da miyagun kwayoyi a tsakanin matasa da ma sauran mutane.
Buhari ya kafa kwamitin ne a dakin taron sha'anin kasuwanci dake fadar sa, Aso Rock, Abuja
Ya bayyana cewar kwaya ta zama daya daga cikin manyan kalubale ga lafiyar 'yan kasa.
Sannan ya kara da cewar yanzu haka Najeriya na daga cikin kasashen duniya da yawan adadin masu amfani da miyagun kwayoyi ke karuwa.
Kazalika, ya bayyana cewar rahoton da hukumar hana sha da safarar miyagun kwayoyi (NDLEA) ta fitar na adadin kwalaben kodin da ake sha kullum a Kano da yankin kudu maso yamma kadai sun matukar tayar masa da hankali.

Source: Twitter
"Wannan wani lamari ne sake bukatar a bashi kulawa ta gaggawa, a saboda haka dole mu dauki mataki," a cewar sa.
"Matasa da dama sun daina zuwa makaranta saboda amfani da miyagun kwayoyi. Amfani da miyagun kwayoyi a tsakanin direbobi na haddasa hatsari. Kwayoyin da aka fi amfani da su a Najeriya sun hada da giya, sigari, gahawa, tramol, kodin da sauran su.
DUBA WANNAN: Kotu ta tisa keyar tsohon gwamna Dakingari da wasu mutane biyu kurkuku
"Yau ta zama watarana da muka kara gyara damara wajen kokarin gyara babbar matsalar dake barazana ga zaman lafiya da cigaban jama'ar wannan lokaci da wadanda zasu bayansu," a kalaman shugaba Buhari.
An kafa kwamiti daya karkashin uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, yayin da aka kafa dayan jagorancin Birgediya janar Buba Marwa (mai ritaya).
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng