Karan bana maganin zomon bana: Jama’an Kano sun lakada ma ma’aikacin NEPA dan banzan duka

Karan bana maganin zomon bana: Jama’an Kano sun lakada ma ma’aikacin NEPA dan banzan duka

Wasu ma’aikatan kamfanin wutar lantarki ta jahar Kano, KEDCO, sun ci dan banzan duka a hannun jama’an unguwar Sharada dake cikin garin Kano saboda zarginsu da suke yi da yanke musu wuta ba bisa ka’ida ba, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Majiyar Legit.com ta ruwaito kaakakin kamfanin, Muhamamd Kandy a tabbatar da faruwar lamarin, sai dai yace tuni aka garzaya da ma’aikatan kamfanin nasu zuwa asibiti sakamakon jikkatan da suka yi a sanadiyyar dukan da suka sha.

KU KARANTA: An bindige mutane 5 yan gida daya a wani hari da miyagu suka kaima banki

A cewar kaakaki Kandi, ma’aikatan da suka karbi kida sun hada da Ali Muhammad, Abdulkadir Waziri da wata ma’aikaciya mace wanda bayan dukanta da aka yi aka kusa tube mata kayanta tsirara, sai dai yace sun yi mamakin haka saboda suna baiwa unguwar wutar awanni ashirin a jere a duk rana.

Karan bana maganin zomon bana: Jama’an Kano sun lakada ma ma’aikacin NEPA dan banzan duka
KEDCO
Asali: UGC

“Duk masu hannu cikin cin mutuncin nan ba zasu sha ba, ba zamu bari wasu su yi mana barazana ba, haka zalika ba zamu daina gudanar da aikinmu kamar yadda doka ta tanadar ba kawai don wasu jama’a na cin zalin ma’aikatanmu.

“Tuni kamfanin KEDCO ya shigar da kara gaban Yansanda don daukan matakin daya dace, muna fata Allah Yasa ayi mana adalci a cikin wannan lamari.” Inji shi.

Daga karshe kaakakin yayi kira ga ma’aikatan KEDCO dasu jajirce wajen gudanar da aikinsu ba tare da jin tsoro ba, da kuma gudanar da aikin cikin bin dokokin kamfanin da tsare tsarenta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel