Taron dangi ba zai razana mu ba ko kadan - APC

Taron dangi ba zai razana mu ba ko kadan - APC

Magoya bayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun mayar da martani ga matakin da hadakar jam'iyyun adawa suka zartar na marawa dan takarar babbar jam'iyyar adawa ta kasar wato Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar baya a zaben 2019.

Tun a watan Yulin da ya gabata ne jam'iyyu sama da 40 suka hade tare da jam'iyyar PDP da zummar kwace ragamar mulki daga hannun Shugaba Buhari da APC.

A makon da ya gabata shugaban kungiyar sabuwar APC wato rAPC, Injiniya Buba Galadima ya bayyana cewa sun yanke shawarar marawa Atiku Abubakar baya ne saboda Shugaba Buhari ya gaza aiwatar da abin da aka zabe shi a kai.

Taron dangi ba zai razana mu ba ko kadan - APC
Taron dangi ba zai razana mu ba ko kadan - APC
Asali: Depositphotos

Sai dai kalaman na Buba Galadima ya fuskanci taron dangi daga wasu 'ya'yan Jam'iyyarta APC da ke cewa matakin da hadakar jam'iyyun ta dauka ko kadan bai girgizasu ba.

Ministan wasanni da harkokin matasa, Barrister Solomon Dalung, ya bayyana gamayyar jam'iyyun da taron guda ba zai iya huda fata ba.

KU KARANTA KUMA: 2019: Gwamnonin 9 masu mulki, da sabbin yan takara 20 ne za su yi takarar gwamna a APC - Oshiomhole

Barrister Solomin ya kuma yi watsi da zarge-zargen da wasu ke yi cewa dan takarar Jam'iyyar adawa ta PDP ya razana su.

Ya ce su hakarsu ce ta cimma ruwa, don wannan dama ce ta Atiku ya fito ya yi wa 'yan kasar bayani tasirin da ya yi a shekaru takwas da ya yi wa tsohon shugaba Olesugun Obasanjo mataimaki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel