Atiku ya fadi asalin karamar hukuma da jihar arewa da kakanninsa su ka fito

Atiku ya fadi asalin karamar hukuma da jihar arewa da kakanninsa su ka fito

A jiya, Litinin, ne dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya shaidawa dumbin jama'ar da su ka halarci taron kaddamar da yakin neman zabensa a Sokoto cewar za a iya siffanta shi da 'komai da ruwanka'.

Atiku tare da jiga-jigan 'ya'yan jam'iyyar PDP sun isa jihar ta Sokoto a jiya domin kaddamar da yakin neman zabensa.

Da yake gabatar da jawabi a wurin taron, Atiku ya bayyana cewar kakanninsa sun fito ne daga garin Wurno, tare da sanar da cewar shi cikakken bafulatani ne.

Atiku ya fadi asalin karamar hukuma da jihar arewa da kakanninsa su ka fito

Atiku ya fadi asalin karamar hukuma da jihar arewa da kakanninsa su ka fito
Source: Facebook

DUBA WANNAN: A bamu makamai mu yaki 'yan ta'adda - Babban Sarki a Zamfara ya roki Buhari

"Ina kira gare ku da kar ku sake yarda da mutumin da zai ce ma ku shanu 150 gare shi bayan ya shafe tsawon shekaru yana kiwo. Ina da shanu sun fi dubu.

"Ni dan kasuwa ne a bangare daban-daban, tamkar komai da ruwanka na ke. Ina noma, kiwo, sannan a baya na yi aikin gwamnati. Saboda haka na fi kowanne dan takara cancanta na mulki Najeriya ko don inganta rayuwar matasa da ke shan wahala saboda rashin aikin yi," a kalaman Atiku.

Atiku ya kara da cewar ya ce ya zama tilas jama'a su fito domin su yi amfani da kuri'unsu wajen kayar da gwamnatin da ta sa jama'a cikin talauci da yunwa.

Yayin taron, shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Uche Secondus, ya mika tuta ga 'yan takarar kujerar gwamna a yankin arewa maso yamma.

Daga cikin manyan 'ya'yan jam'iyyar PDP da su ka halarci taron kamfen din akwai; Goodluck Jonathan, Namadi Sambo, Bukola Saraki, Yakubu Dogara, Rabi'u Musa Kwankwaso, Sule Lamido, Aminu Waziri Tambuwal, da sauran su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel