Babban magana: Kotu ta daure wasu mutane biyu saboda satar wayar alkali

Babban magana: Kotu ta daure wasu mutane biyu saboda satar wayar alkali

Wani alkalin kotun Majistare a Ilorin ya bayar da umurnin a bawa wasu maza biyu, Samson John da Ayodele Oluwagbemiga masauki a gidan dan Kande saboda satar wayar sallular wani alkali.

Mai sharia'a Ibijoke Olawoyin ya bayar da umurnin ne bayan an gurfanar da mutane biyu inda ake zarginsu da hadin baki, shiga gida ba izini da aikata sata.

Ms Olawoyin ta dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 20 ga watan Disamba.

Babban magana: An gurfanar da wasu a kotu saboda sace wayar alkali

Babban magana: An gurfanar da wasu a kotu saboda sace wayar alkali
Source: Twitter

Da farko, mai shigar da kara, Alhassan Jibrin ya shaidawa kotu a ranar 22 ga watan Nuwamba ne wani Usman Olayinka da ke aiki a kotu a Ilorin ya shigar da kara a ofishin 'yan sanda da ke Ilorin.

DUBA WANNAN: Shugabanin kabilar Yarabawa sun goyi bayan Atiku

Mr Jibrin ya ce wanda ya shigar da karar ya yi ikirarin cewa wanda ake zargin wanda mai gadi ne a gidan alkalin tare da wani abokinsa sun shiga cikin gidan alkalin suka sace wayarsa kirar Samsung Galaxy wanda kudinsa ya kai N300,000 da wasu gwalagwalai da kuma kudi N10,000.

Mai shigar da karar ya ce yayin binciken 'yan sanda wanda ake zargin ya bayyana cewa ya yi amfani da makulin dakin mai gadin wajen bude babban kofar gidan daga nan kuma ya shiga dakin alkalin ya sace kayayakin.

Ya kuma ce ya sayar da watan kan kudi N10,000 ga wani Micheal a kauyen Asoka a Benue sannan ya sayar da gwalagwalen a kan kudi N7,000 ga mutum na biyu da ke tuhuma da ke zaune a Fakeye Street, Basin, Ilorin.

Mai shigar da karar ya ce laifin da suka aikata ya ci karo da sashi na 97, 348, 288 da 317 na Penal Code.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel