Ba bu wata wahala da za a fuskanta, akwai wadataccen Man Fetur a Najeriya - NNPC

Ba bu wata wahala da za a fuskanta, akwai wadataccen Man Fetur a Najeriya - NNPC

A yayin da tsanani na karanci da wahalhalun Man Fetur ta kasance tamkar wata al'ada a fadin kasar a duk karshen shekara, kamfanin man fetur na kasa watau NNPC ya yiwa al'ummar Najeriya Albishir kan cewa hakan ba za ta sabu ba a bana.

Kamfanin na NNPC a jiya Litinin ya bayar da sanarwar cewa, ba bu wani cuzguni da al'ummar kasar nan za ta fuskanta ta fuskar karanci da wahalhalun man fetur a karshen shekarar bana duk da barazana da kuma wa'adin da 'yan kasuwar man fetur suka gindayawa gwamnatin tarayya.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, kamfanin ya bayyana cewa a halin yanzu ya dukufa wajen samar da sulhu tsakanin 'yan kasuwar da kuma cibiyoyon gwamnatin tarayya masu ruwa da tsaki kan harkokin man fetur a kasar nan domin tabbatar da biyan bukata ga Dillalan man fetur da ke fadin kasar nan.

A yayin haka kamfanin ya yi kira na neman kwanciyar hankalin al'ummar kasar nan da cewa, akwai wadataccen makamashin man fetur cikin kasar nan da ba zai yanke ba har zuwa wani lokaci mai tsayin gaske.

Shugaban kamfanin Man Fetur na kasa; Dakta Maikanti Baru

Shugaban kamfanin Man Fetur na kasa; Dakta Maikanti Baru
Source: Depositphotos

Rahotanni sun bayyana cewa, a karshen makon da ya gabata kungiyar dillanlan man fetur ta kasa, ta bai wa gwamnatin tarayya wa'adin kwanaki bakwai kan tabbatar da sauke nauyin bashin dukkanin tallafin man fetur da ke kanta a halin yanzu.

Dillalan na man fetur karkashin kungiyar Major Oil Marketers Association of Nigeria, Depot and Petroleum Products Marketers da kuma kungiyar Independent Petroleum Products Importers, sun yi barazanar janye duk wani aikace-aikacen su a fadin kasar nan muddin gwamnatin tarayya ta gaza wajen biyan bukatun su.

KARANTA KUMA: Boko Haram: Mayaƙa sun ƙone wata babbar Gonar Shinkafa a jihar Borno

Sai dai yayin tuntubar manema labarai, babban Manajan kamfanin NNPC akan harkokin hulda da al'umma, Ndu Ughamadu, ya bayyana cewa, al'ummar kasar nan ta kwantar da hankalinta domin kuwa wannan barazana ba za ta yi tasiri ba kasancewar wadattacen man fetur da kamfanin ya riga da tanadin sa.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, Mista Ughamadu ya bayyana cewa akwai kyakkyawan zato dangane da samun madogara guda ta sulhu tsakanin kungiyoyin da kuma gwamnatin tarayyar Najeriya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel