An dakatar da Hakimai 2 saboda shirya taron yi wa Buhari addu’o’i a jihar Gombe

An dakatar da Hakimai 2 saboda shirya taron yi wa Buhari addu’o’i a jihar Gombe

Rahotanni sun kawo cewa mai martaba sarkin Deba ya dakatar da wasu Hakimai biyu da ke karkashin masarautar sa sakamakon gudanar da taron yi wa shugaban Kasa Muhammadu Buhari addu’o’i a garuruwan su da suka yi.

Hakiman da aka dakatar sune, hakimin Garin Mallam Alhaji Julde da Ummaru Bappayo na garin Wajari.

A wasikar da sakataren masarautar Deba, Saidu Mele ya mika wa Hakiman, ba a bayyana dalilin da ya sa aka dakatar da su ba amma an ce daga wannan rana su kwabe rawaninsu su har sai sun ji daga masarautar.

An dakatar da Hakimai 2 saboda shirya taron yi wa Buhari addu’o’i a jihar Gombe
An dakatar da Hakimai 2 saboda shirya taron yi wa Buhari addu’o’i a jihar Gombe
Asali: UGC

“Daga yau an dakatar da ku daga ci gaba da sarautar garuruwan ku.”

Julde ya bayyana wa majiyarmu ta Premium Times cewa yana da yakinin cewa gwamnatin jihar ne ta sa ayi musu haka.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Majalisar dokoki ta aika sammaci ga jakadan Amurka

Ita ko masarautar Deba karyata wannan korafi da hakiman suka yi tayi inda ta ce babu sarkin da ya dakatar da wani hakimi saboda wai ya shirya taron yi wa Buhari addu’o’i, su dai su bayyana laifukan su na gaskiya.

Shima Kwamishinan Yada Labarai na jihar Umar Nafada, ya bayyana cewa bashi da masaniya game da wannan zance na dakatar da wasu hakimai don sun yi wa Buhari addu’o’i.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng