Jirgin kasa ya mirtsike wani matsahi a Abuja

Jirgin kasa ya mirtsike wani matsahi a Abuja

Jirgin kasa ya mirtsike wani mutum mai matsakaicin shekaru, da ya zuwa yanzu ba a gano ko waye ba, a yankin Phikwore da ke unguwar Kubwa a birnin tarayya, Abuja.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya rawaito cewar matashin ya bar wata takarda kafin daga bisani ya je ya kwanta a kan diga domin jirgin kasa ya bi ta kansa.

NAN ta bayyana cewar lamarin ya faru ne a yau, Litinin, da misalin karfe 12:45 na rana.

Matashin ya bar wasika a cikin wata jakarsa da ya ajiye a gefen digar jirgin da ya kwanta.

Wasu shaidun gani da ido da su ka yi magana da NAN sun ce matashin ya bar rubutaccen sako ga matar sa da yaransa kamar haka; "ku yafe min, saboda bani da kudin da zan iya daukar nauyin ku."

Jirgin kasa ya mirtsike wani matsahi a Abuja

Jirgin kasa
Source: Depositphotos

Ya zuwa yanzu dai ba a iya gano suna ko daga inda mutumin ya fito ba.

DUBA WANNAN: Wanzami ya farke cikin wani mutum da ya je zance wurin wata budurwar a Katsina

Kakakin hukumar kula da harkokin jirgin kasa, Mista Niyi Ali, ya tabbatar da faruwar lamarin ga NAN tare da bayyana cewar har yanzu suna binciken dalilin mutumin yin abinda ya aikata.

"Za mu yi bincike domin gano abinda zai sa matashi ya kwanta a titin jirgin kasa domin ya bi ta kansa, ya mutu," a cewar Ali.

Har ya zuwa lokacin buga wannan rahoto, ba a dauke gawar matashin daga gefen digar jirgin kasan ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel