2019: Atiku ya zayyano matakan da zai bi na maida Boko Haram tarihi

2019: Atiku ya zayyano matakan da zai bi na maida Boko Haram tarihi

‘Dan takarar Shugaban kasa na zaben 2019 a Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar yai dogon rubutu a kwanan nan a Jaridar This Day inda ya bayyana yadda zai bi ya kawo karshen Boko Haram idan har ya samu mulkin kasar nan.

2019: Atiku ya zayyano matakan da zai bi na maida Boko Haram tarihi
Atiku zai tsaida amfani da kudin tsaro da Gwamnoni su ke yi
Asali: Depositphotos

Atiku Abubakar ya bayyana cewa zai yi wa tsarin kasar nan garambawul, wanda da zarar an yi hakan, Boko Haram za ta rasa tubulin dafawa a Yankin Arewa maso Gabas. Atiku yace mafi yawan ‘Yan ta’addan, mutanen gida ne.

Haka kuma Atiku ya bayyana cewa zai duba tattalin arzikin Yankin da wannan rikici ya shafa (watau Borno, Yobe da Adamawa) da idanun basira domin ganin an takaita shiga cikin Kungiyar ta’addan domin samun abin Duniya.

KU KARANTA: Gudaji Kazaure ya nemi a tsige su Buratai domin kawo karshen Boko Haram

‘Dan takarar na PDP yake cewa zai duba silar yadda Kungiyar ta zama ta ta’adda bayan kashe Shugaban ta sannan kuma ya bayyana cewa Borno da Yobe su na cikin Jihohin da ake samun yara marasa zuwa Makarantar Boko a ban kasa.

Har wa yau, Atiku ya nuna cewa cewa zai yi bakin kokarin sa wajen ganin an ba Sojojin Najeriya duk gudumuwar da su ke bukata. Ya kuma jadadda cewa zai hana barnar da Gwamnonin Kasar su ke yi da dukiyar Gwamnati da sunan tsaro.

A rubutun na Atiku, ya numa cewa zai ba Mata da Matasa dama a Gwamnati musamman a Majalisa da mukaman zartarwa da kuma hanyar gina ayyukan more rayuwa. Atiku ya kuma soki korar Malaman Makaranta da ake yi daga aiki a Kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel