Manyan tsare-tsaren da Buhari ya kawo a wajen fannin gona

Manyan tsare-tsaren da Buhari ya kawo a wajen fannin gona

Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari tayi gagarumar kokari a bangaren noma. Wata Jaridar Kasar nan ta kawo irin nasarorin da aka samu a Najeriya a cikin shekaru 3 da su ka wuce na Gwamnatin nan.

Manyan tsare-tsaren da Buhari ya kawo a wajen fannin gona

Babban Ministan harkokin gona na Najeriya Audu Ogbeh
Source: Depositphotos

A farko dai, kudin shigar da Najeriya ta ke samu da kayan gona sun haura Dala Biliyan 45 a yanzu. Shugaba Buhari ya kawo tsarin raba abinci a makarantu, hakan ya bunkasa harkar noma da kasuwanci tare da kuma inganta harkar ilmi a Kasar.

Gwamnatin Buhari ta kawo tsarin nan na LIFE watau “Livelihood Improvement Family Enterprises” wanda aka shirya domin samawa mutanen karkara abin yi ta hanyar noma. Wannan tsari zai samawa dinbin matasa sana’a a cikin Kauyuka.

Akwai kuma wani tsari da babban bankin Kasar na CBN ya kawo wanda ake kira “Anchor Borrowers Programme”. A wannan shiri na ABP, an ba manoma aron kudi domin noman shinkafa da sauran hatsi a Jihohin Kebbi, Zamfara da sauran su.

KU KARANTA: Ya kamata a daina nada tsofaffin mutane a matsayin Ministoci - Gbor

Ma’aikatar harkokin ruwa ta kuma yi kokari wajen inganta noman rani a halin yanzu. Haka kuma bankin Manoma watau BOA ya kawo sababbin tsarin ba Manoma bashi. Yanzu dai Bankuna har da irin su AfdB sun ba ‘Yan Najeriya bashi.

Gwamnatin Shugaba Buhari ta kashe Biliyoyin kudi wajen shigo da kayan noman zamani wanda su ka hada da manyan motocin gona akalla 18, 000. An kaddamar da wannan shiri da ake kira Agricultural Equipment Hiring Enterprise ne a Abuja.

Har wa yau an samu takin zamani ta tsarin ‘Presidential Fertilizer Initiative na PFI a Najeriya. Wannan ya sa taki yayi sauki kuma cikin kudi mai rahusa. Yanzu kamfanonin Najeriya 11 ne su ka dawo su na aikin hada takin zamani a Gwamnatin Buhari.

Ban da wadannan dai akwai wasu dinbin tsare-tsare da aka kawo wanda su ka sa Najeriya ke fita da kayan abinci har kasashen ketare tare da bunkasa harkar noman shinkafa a cikin gida da sauran su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel