Muhimman abubuwa 6 da ya kamata ku sani game da marigayi Dr Fredrick Fasehun

Muhimman abubuwa 6 da ya kamata ku sani game da marigayi Dr Fredrick Fasehun

Dr. Frederick Fasehun wanda ya kafa kungiyar Yarabawa ta Oduduwa Peoples Congress (OPC) ya rasu a Asabar 1 ga watan Disambar shekarar 2018.

Dr Fredrick Fasehun mai shekaru 80 ya rasu ne a asibitin koyarwa na Jami'a Legas (LASUTH) da ke Ikeja inda ya ke samun kulawa kan wata cuta da ba a bayyana ba.

Shafin adana bayanai na Wikipedia ya nuna cewar an haifi Dr Dr. Frederick Fasehun ne a shekarar 1938 a birnin Ondo.

Muhimman abubuwa 6 da ya kamata ku sani game da marigayi Dr Fredrick Fasehun
Muhimman abubuwa 6 da ya kamata ku sani game da marigayi Dr Fredrick Fasehun
Asali: Twitter

Legit.ng Hausa ta tattaro muku wasu muhimman bayanai game da marigayin:

1. Baya ga kasancewarsa likita da kuma dan gwagwarmaya, Dr Fredrick Fasehun kuma ya mallaki Otel

2. Ya fara karatunsa ne a Kwallejin Blackburn sannan ya cigaba a Jami'ar koyan aikin likitanci na Aberdeen inda ya kware a fannin tiyata.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun yi karin haske a kan bayyanar wasu bakin 'yan bindiga a Sokoto

3. A shekarar 1976 ya garzaya kasar Sin inda ya yi karatun likitancin Acupuncture wadda ake tsira kananan allurai a sassan jikin mutum domin magance wasu cututtuka da suka hada da ciwon kai, hawan jini, ciwon gabobi, tari da sauransu.

4. A shekarar 1977, ya kafa sashin likitancin Acupuncture a asibitin koyarwa na Jami'ar Legas amma bayan shekara guda a 1978 ya yi murabus sannan ya kafa asibitinsa, Besthope Hospital and Acupunture Centre a Legas wadda itace asibiti na farko a Afirka da ke amfani da likitancin Acupunture.

5. Ya kafa kungiyar OPC ne domin ganin kallubalantar soke zaben shugabancin kasa da akayi na 12 ga watan Yunin 1993 wadda Cif Moshood Kashimawo Olawale Abiola ya lashe.

6. An garkame Dr Fasehun a kurkuku na tsawon watanni 19 daga Disambar 1996 zuwa Yunin 1998 a zamanin mulkin tsohon shugaban Najeriya na mulkin Soja, Sani Abacha. An sake shi daga kurkuku kwanaki 18 bayan rasuwar Abacha.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel