Lamarin Atiku na neman izinin shiga kasar Amurka abu ne na sirrance - Jakadan Amurka

Lamarin Atiku na neman izinin shiga kasar Amurka abu ne na sirrance - Jakadan Amurka

A jiya Juma'a Ofishin jakadancin kasar Amurka da ke jihar Legas, ya bayyana cewa dukkanin al'amurra da suka shafi neman izini ko bayar da lasisin shiga kasar Amurka ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ababe ne na sirrance da kuma rikon amana.

Babban ofishin kamar yadda rahotanni suka bayyana ya tabbatar da cewa, wannan lamari na neman izini tare da bayar da lasisin shiga kasar Amurka boyayyen lamari ne da gwamnatin kasar Amurka ba za taba fayyace wannan sirri ko cin amana a bainar al'umma.

Kakakin ofishin jakadancin da ke jihar Legas, Brussel Brooks, shine ya bayyana hakan da cewa akwai bukatar matsanancin sirri kan wannan lamari na neman izini ko bayar da lasisi shiga kasar Amurka ga Atiku ko waninsa ba tare da duba izuwa martaba ko karamcinsa a tsakankanin al'umma.

Lamarin Atiku na neman izinin shiga kasar Amurka abu ne na sirrance - Jakadan Amurka

Lamarin Atiku na neman izinin shiga kasar Amurka abu ne na sirrance - Jakadan Amurka
Source: Twitter

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, Mista Brooks ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da manema labarai bayan halartar taron harkokin ilimi da suka shafi kasar nan da aka gudanar a birnin Ibadan na jihar Oyo.

Lamarin da ke zuwa bayan kimanin tsawon sa'o'i 24 inda gwamnatin tarayyar Najeriya ta kirayi gwamnatin kasar Amurka kan sanya fa'ida ta hankali dangane da bayar da lasisin shiga ga dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP.

KARANTA KUMA: Jam'iyyu 73 za su fafata takarar shugaban kasa a zaben 2019 - INEC

A sanadiyar haka jakadan na kasar Amurka ya gargadi gwamnatin Najeriya, 'yan takara da dukkanin 'yan siyasa akan kauracewa tsoma bakin su da kuma gujewa katsalandan cikin lamarin da ba ya jinginuwa izuwa gare su.

Yayin jaddada matsayarsa da kuma akida ta gwamnatin kasar Amurka, Mista Brooks ya bayyana cewa akwai matsananciyar amana da rikon sirri mai girman gaske kan lamari na neman izinin ko bayar da lasisin shiga kasar Amurka ga Atiku ko kuma waninsa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel