'Yan sanda sun cafke wani gawuratacen dillalin sassan jikin dan adam

'Yan sanda sun cafke wani gawuratacen dillalin sassan jikin dan adam

- Jami'an 'yan sanda sunyi nasarar damke wani mutum dauke da idanun dan adam a jihar Niger

- Wanda aka kama din ya ce shi dai dan sako ne kawai kuma bai san abinda ake aikatawa da shi ba

- An gano cewar ya kwashe shekaru biyar yana wannan sana'an amma sai jiya asirinsa ya tonu

'Yan sanda sun cafke wani gawuratacen dilalin sassan jikin dan adam
'Yan sanda sun cafke wani gawuratacen dilalin sassan jikin dan adam
Asali: Twitter

'Yan sanda sunyi nasarar kama wani dalilin sassan jikun mutane a jihar Niger dauke da idanun dan adam da aka kwakwule daga wata gawa.

An kama Shuaibu Ibrahim dan asalin kauyen Safiu da ke karamar hukumar Toto na jihar Nasarawa a yayin da 'yan sandan yankin Gawu Babangida a karamar hukumar Gurara ke sinitiri a unguwar.

Jami'an yan sandan sun ce an ciro idanun ne daga gawar wani mutum da ya mutu sakamakon rikicin da akayi tsakanin 'yan kabilar Igbira da Bassa a jihar Nasarawa.

DUBA WANNAN: Bidiyon Ganduje: 'Yan majalisun tarayyar APC na jihar Kano sun fadi ra'ayoyinsu

Yan sandan sun ce wanda ake zargin ya kwashe shekaru biyar yana safarar sassan jikin mutane amma sai jiya asirinsa ya tonu.

Wanda ake zargin ya ce wani Ojo ne ya bashi idanun domin ya je ya sayar a jihar Niger kan kudi N250,000.

Wand ake zargin ya tabbatarwa manema labarai cewa shi kawai dan sako ne tsakanin Ojo da masu sayan sassan jikin mutanen.

"Ni aiki na kawai shine in kai sassan jikin da Ojo ya bani zuwa jihohin arewa inda masu sayan za su karba. Muna samun kudi sosai daga wannan kasuwancin amma ni ban san abinda masu sayan su keyi da sassan jikin ba," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel