Layukan waya sun karu zuwa 165m a watan Oktober - NCC

Layukan waya sun karu zuwa 165m a watan Oktober - NCC

Hukumar Sadarwa na Najeriya (NCC) ta ce adadin layyukan waya da 'yan Najeriya ke amfani dashi sun karu daga 162,058,918 a watan Satumba zuwa 165,239,443 a watan Oktoban shekarar 2018.

A cewar kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN), NCC ta bayar da wannan sanarwan ne a mujjalar wata-wata da take wallafawa a shafinta na yanar gizo a jiya Alhamis.

Punch ta ruwaito cewa hukumar ta ce layyukan wayoyin sun karu da 3,180,525 daga 162,058,918 da ake da su a watan Satumba.

Layukan waya sun karu zuwa 165m a watan Oktober - NCC
Layukan waya sun karu zuwa 165m a watan Oktober - NCC
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: An kara samun sansanin horon soji na bogi a jihar PDP

Rahoton ya ce a cikin layyukan wayan da ake amfani da su 165,239,443, tsarin GSM ya tantance 164,865,417 a watan Oktoba 2018.

Hakan na nuna cewa tsarin na GSM ya samu karin masu hulda da shi 3,179,670 a watan Oktoba idan a maimakon 161,685,747 da aka samu a watan Satumba.

NCC ta ce ana samun karuwar masu amfani da layyukan waya da 2.27% duba da cewa a Satumba ana da 115.76 amma a Oktoba an samu 118.03.

A wani rahoton, Legit.ng ta kawo muke cewa sojojin Najeriya sun gano sansanin horas da sojoji na bogi a Nonwa Gbam da ke karamar hukumar Tai na jihar Rivers.

Sai dai gwamnan jihar, Nyesom Wike ya zargi Hukumar Sojin Najeriya da yunkurin tayar da zaune tsaye a jihar inda ya ce 'yan banga jihar ke horas wa kuma tayi hadin gwiwa da 'yan sanda da wasu hukumomin tsaro kafin aka fara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel