Wadanda suka sauya sheka daga APC sun yi danasanin marawa Buhari baya a 2015

Wadanda suka sauya sheka daga APC sun yi danasanin marawa Buhari baya a 2015

Wasu daga cikin mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) daga jihohin Kano, Katsina da kuma Kaduna da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun bayyana cewa sun yi danasanin zabar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a 2015.

Legit.ng ta tattaro cewa shugaban kungiyar, Mallam Yusuf Maikano, ya bayyana zabar shugaba Buhari a zaben 2015 a matsayin kuskure.

Wadanda suka sauya sheka daga APC sun yi danasanin marawa Buhari baya a 2015

Wadanda suka sauya sheka daga APC sun yi danasanin marawa Buhari baya a 2015
Source: Depositphotos

Vanguard ta ruwaito cewa Maikano yayi korafin cewa gwamnatin Buhari ta janyo wahalar rayuwa a Najeriya, musamman a arewa.

Ya ce: “Muna jin tarin yaudarar da Shugaba Buhari yayi mana ta hanyar kin cika alkawaran kamfen da ya dauka a 2015 sannan yanzu gwamnatinsa na ta ikirarin karya da kuma lissafo sabbin alkawara, maimakon ya ba da hakuri akan gazawarsa.”

KU KARANTA KUMA: Buhari ya dawo Najeriya bayan halartar taro a kasar Chadi

A wani lamari na daban mun ji cewa 'Yan majalisar wakilai na tarayya na APC sun ki cewa uffan a kan fayafayen bidiyon da aka saki da ke nuna Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na karbar daloili daga hannun 'yan kwangila da ake zargin rashawa ce.

Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan majalisar na jam'iyyar APC guda bakwai sun hadu ne a harabar majalisar tarayyar domin jadada goyon bayansu ga gwamnan jihar na Kano.

Sai dai bayan sun kammala karanto jawabinsu inda suka jinjina wa gwamnan kan nasarorin da ya samu tun kama aiki a shekarar 2015, yan jarida sun jefa musu tambayoyi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel