Bacewar biliyoyin naira: Majalisar dattawa za ta bincike hukumar kula da tashoshin ruwa

Bacewar biliyoyin naira: Majalisar dattawa za ta bincike hukumar kula da tashoshin ruwa

Majalisar dattawa ta ba kwamitinta da ke kula da Zirga-zirgar Jiragen Ruwa (NPA) kwanaki uku don ya gano inda wasu tarin kudade har naira biliyan 177 da NPA ta ki zubawa a aljihun gwamnatin tarayya suke.

Wani dan kwamitin ne mai suna Sanata Mohammed Hassan ya ja hankalin majalisar cewa akwai wasu naira biliyan 177 da hukumar NPA ba ta zuba a asusun gwamnatin tarayya ba.

Daga nan sai ya nemi da a gaggauta binciken shin har yanzu kudaden sun a a hannun NPA, ko kuwa ina suka makale?

A ranar Laraba, 28 ga watan Nuwamba ne Hassan ya ce NPA ta tara kudaden shiga har naira bilyan 303, wadanda ya ce ta kashe naira bilyan 125 a ciki, amma ba ta zuba sauran naira biliyan 177 a cikin asusun gwamnatin taratyya ba.

Bacewar biliyoyin naira: Majalisar dattawa za ta bincike hukumar kula da tashoshin ruwa

Bacewar biliyoyin naira: Majalisar dattawa za ta bincike hukumar kula da tashoshin ruwa
Source: UGC

Hassan ya ce duk wani kokari da majalisar dattawa ta yi domin hukumar NPA ta bayyana mata inda kudaden suke, ya ci tura.

KU KARANTA KUMA: Rudunar soji ta kai ziyarar ta’aziya ga uwargidan sojan da ya mutu (hotuna)

Ya ce wata bakwai kenan su na neman a yi musu inda kudaden suka makale, amma an yi watsi da bukatar ta su.

Daga nan sai Shugaban Majalaisar Dattawa. Bukola Saraki ya bada umarnin cewa kwamitin ya gaggauta gano inda kudaden suka shige a cikin kwanaki uku.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel