Ma su garkuwa da mutane sun sace mataimakin kwanturola na kwastam

Ma su garkuwa da mutane sun sace mataimakin kwanturola na kwastam

An kama wasu 'yan kungiyar masu garkuwa da mutane su 7 bisa zarginsu da sace mataimakin kwanturola a hukumar kwastam, Justina Tanko, tare da kisan wani dan kasuwa, Chukwubuikem Ezenkwu.

Wadanda ake zargin su ne; Godspower Keenom, Zigabari Voonu, Oludofin Yakubu, Jastis Afangide, Dale Keliaga, Maxwell Barindom, da Tordi Barinaa. Rundunar babban sifeton rundunar 'yan sanda ta martanin gaggawa ce bisa jagorancin Abba Kyari ta yi nasarar cafke mutanen a yankin Onne a jihar Ribas.

Rahotanni sun bayyana cewar ma su laifin sun karbi miliyan N5m kudin fansa kafin su saki jami'ar hukumar kwastam, Tanko.

Masu garkuwa da mutanen sun kashe dan kasuwar tare da jefa gawar sa a cikin wani tafkin ruwa duk da sun karbi miliyan N2.5m kudin fansa.

Ma su garkuwa da mutane sun sace mataimakin kwanturola na kwastam
Shugaban hukumar kwastam tare da jami'ansa
Asali: Depositphotos

A wani labarin mai kama da wannan da Legit.ng ta kawo ma ku, kun ji cewar rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Sokoto ta sanar da cewar ta kama wani mutum mai suna Ibrahim Dangaladima da ke yin sojan gona a matsayin babban sifeton rundunar 'yan sanda na kasa (AIG).

DSP Cordelia Nwawe, kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, ne ya bayyana hakan a yau, Laraba, a garin Sokoto.

Nwawe ya kara da cewar Dangaladima ya dade a cikin jerin mutanen da hukumar 'yan sanda ke nema ruwa a jallo bisa laifukan damfara da sojin gona a cikin watanni hudu da su ka wuce.

DUBA WANNAN: Badakalar kudi: An gurfanar da Farfesa Fatima ta makarantar Dadin-Kowa

"Karyar sa ta kare ne ranar Juma'a, 23 ga watan Nuwamba, bayan yin karyar cewar shine babban sifeton rundunar sanda tare da yin alkawarin samar da aiki ga aiki ga yaran wasu 'yan kasuwa.

"Ya nemi a bashi N482,500 ga duk takardar aiki ta ASP da N222,000 ga duk takardar aiki a matakin Inspekta."

"Bayan ya shiga hannu, ya tabbatar da cewar ya kai tsawon shekaru 5 yana aikata irin wannan damfara ga jama'a," a cewar Codelia.

Kazalika rundunar 'yan sandan ta yi bajakolin wani kwararren barawon mota mai suna Surajo Muhammad, dan asalin yankin Arkila a jihar.

A cewar kakakin, an kama Suraja a hannu yayin da yake tsaka da yunkurin sace mota a masallacin Shehu.

Rundunar 'yan sandan jihar ta ce ta dade tana neman Suraja kafin daga bisani ta samu nasarar kama shi, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel