Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya isa Maiduguri
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya isa Maiduguri, babbar birnin jihar Borno don kaddamar da bude taron ma'aikatan hukumar soji na shekara-shekara da ke gudana a jihar.
Legit.ng ta tattaro cewa hadimin shugaba Buhari na musamman a shafin zumunta, Bashir Ahmad ya wallafa hakan a shafinsa na twitter.
Hadimin shugaban kasar yace da farko an shirya gudanar da taron ne a Benin, babbar birnin jihar Edo.
Da saukarsa a Maiduguri kai tsaye shugaban kasar ya isa filin taron a yankin Maimalari.
A wajen taron shugaban kasa Buhari ya yi jawabi, inda ya yaba ma hukuncin hukumar sojin na mayar da taron Maiduguri daga Benin bayan kisan kiyashin da aka yiwa dakarun sojin kasar a kwanan nan.
Ana sanya ran shugaban zai gabatar da jawabi ga dakarun kasar da ke yaki da kungiyar Boko Haram.
KU KARANTA KUMA: Rabon kwado: Kungiyoyin PDP 145 sun bijirewa Atiku, sun koma bayan Buhari da APC
Ziyarar dai ta zo ne kwanaki kadan bayan 'yan Boko Haram sun kai munanan hare-hare da suka yi sanadiyyar rasa rayukan sojojin kasar kimanin "100" a sansaninsu da ke jihar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng