Harin Metele: Har yanzu ba’a kwashe gawarwakin Sojojin da aka kashe ba
Gawarwakin dakarun Sojin Najeriya da mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram suka kashe na can a barbaje a dajin Metele har yanzu ba’a kwashesu ba, da gawarwakin sojojin sa kai na sibiliyan JTF, inji rahoton jaridar Sahara reporters.
Majiyar Legit.com ta ruwaito akalla dakarun Sojin Najeriya dari da ashirin ne mayakan Boko Haram suka kashe, ciki har da hafsoshin soja guda biyar, a harin kwantar baunan da suka kai ma sansanin Sojoji dake Metele dake cikin karamar hukumar Mobar ta jahar Borno.
KU KARANTA: Yadda Kaakakin majalisa ya tsallake rijiya da baya a farfajiyar majalisa
Bayan wannan hari da mayakan Boko Haram suka kai, an tura dakarun Sojoji su kwaso gawarwakin wadanda aka kashe, amma suma sun ci karo da mayakan Boko Haram, inda suka yi musayar wuta, wanda hakan yasa suka koma baya.
Wani jami’in Soja wanda da shi aka tafi kwasan gawarwakin abokan aikinsu ya bayyana ma majiyarmu cewa sun gamu da wuta daga Boko Haram, inda suka zubar da motocinsu suka tsere da kafafuwansu gudun kilomita hamsin ba tsayawa.
“Mun kwashe kusan gawarwakin Sojoji da na JTF guda dari da ashirin, muna cikin aikin ne sai kwatsam yan ta’addan Boko Haram suka fado mana, suka bude mana wuta ta ko ta ina, sa’annan suka tsere.
“Sojoji da dama sun mutu a sanadiyyar harin, don haka bamu samu daman kwashe gawarwakin da ake aikemu kwashewa ba, muma da muka tsira bamu gama haduwa ba, don haka bamu da cikakken bayani game da adadin Sojojin da aka kashe.” Inji shi.
Wannan asara da rundunar Sojin Najeriya ta samu ya sanya shugaban kasa Muhammadu Buhari fasa zuwa jahar Edo inda zai halarci taron manyan hafsoshin rundunar sojan kasa da aka shirya a Bini, a yanzu mayar da tafiyar tasa zuwa jahar Borno don gane ma idonsa halin s Sojojin Najeriya ke ciki
A wani labarin kuma, rundunar Sojin sama ta bayyana cewa ta kai ma mayakan Boko Haram wani mummunan hari ta amfani da jiragenta na yaki a garin Metele, inda tace ta kashe sama da yan ta’adda dari biyu da goma sha uku.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng