EFCC ta rufe dukkan asusuna, ga iyalina ba abinci - Jigo a PDP ya koka
A yau, Talata, ne tsohon sakataren yada labaran jam'iyyar PDP na kasa, Olisa Metuh, ya shaidawa wata kotun tarayya dake zamanta a Abuja cewar hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta rufe dukkan asusunsa dake bankunan kasar nan.
Metuh ya shaidawa kotun cewar ya yi matukar girgiza bayan ya fahimci cewar hukumar ta bayar da umarnin garkame dukkan asusunsa yayin da ya yi yunkurin taba kudinsa da ke daya daga cikin bankunan da ya ke da asusu.
Ya fadawa alkalin kotun, Jastis Okong Abang, cewar yanzu haka ko iyalinsa ba su da abincin da zasu ci sakamakon kulle asusun nasa da EFCC ta yi.

Asali: Twitter
Metuh na wadannan kalamai ne yayin da yake bayar da shaida a gaban kotun a kan tuhumar da EFCC ke yi ma sa.
DUBA WANNAN: Gwamna Yari ya dakatar da sarakuna hudu a Zamfara
Tsohon kakakin na PDP ya ce, "EFCC ta rufe dukkan asusuna a daren jiya, Litinin, lamarin da ya sa yanzu haka ko abincin da iyalina zasu ci babu a gidana.
"Na yi matukar girgiza da abinda EFCC ta yi gare ni. Ban ma san me zan ce ba.
"Sun rufe min dukkan asusuna dake bankunan kasar nan. A halin yanzu ko kudin sayen kwayar fanadol ko ruwan sha bani da shi."
Metuh ya kara da cewar EFCC ta rufe asusun sa ne saboda tuhumar da take yi masa a kan karbar N400m daga ofishin Sambo Dasuki, tsohon mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro tsaro, ba bisa ka'ida ba tun shekarar 2014.
Ya bayyana mamakinsa a kan wannan mataki da EFCC ta dauka bayan a baya ta kwace dukkan kadarorinsa tare da kwace dukkan kudaden dake hannun wani kamfani da ke kula ma sa da su.
"Sun yi zargin cewar an sace N400. Me yasa ba zasu tsaya iya kan asusun da su ke zargin an yi amfani da shi wajen sace kudaden ba? Ta yaya kenan yanzu zan iya ciyar da iyalina tun da bani da wata hanyar da zan iya taba kudin da nake da su. Ni a shirye nake wannan karar ta kare na fuskanci hukuncin da kotu za ta zartar a kaina," a cewar Metu.
A kwanakin baya ne Metuh ya gabatar da takardun wasu taruka da ya halarta lokacin yana kakakin jam'iyyar PDP tare da yin korafin cewar halartar tarukan ne ya sa ake yiwa rayuwar sa barazana tare da gurfanar da shi saboda jam'iyyar APC da shugaba Buhari na da fushin cewar ya halarci taron.
Hukumar EFCC na tuhumar Metuh tare da wani kamfaninsa da aikata laifuka bakwai da ke da alaka da karbar kudi ta haramtacciyar hanya daga ofishin Sambo Dasuki a ranar 22 ga watan Nuwamba na shekarar 2014.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng