Girgizar kasa ta jikkata mutane 700 a kasar Iran
Rahotanni da ku zuwa mana sun nuna cewa akalla sama da mutane 700 ne suka jikkatta sanadiyar wata girgizar kasa mai karfin maki 6.3 da ta faru a kudancin kasar Iran a ranar Lahadi, shafin BBC Hausa ta ruwaito.
An tattaro cewa annoar girgiza ta fi kamari ne a lardin Kermanshah, inda a bara ma sama da mutane 600 ne suka mutu a wata mummunar girgizar kasa a tsawon shekara 10.
An jiyo motsin kasar a yankuna da dama na kasar, inda aka tattaro cewa akalla mutum guda ne ya rasa ransa a kusa da yankin Kurdistan na kasar Iraki.

Asali: Depositphotos
Sai dai babu rahotannin asarar rayuka a kasar Iran, kuma babu wani rahoto da ke cewa girgizar kasar ta yi wani babban ta'adi.
KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa nake wayar wa da al’umma kai akan yaki da rashawa - Ganduje
Gwamnan lardin da abin ya shafa Houshang Bazvand ya ce: "Kimanin mutum 729 ne suka ji raunuka, 700 an yi musu magani har ma an sallame su...18 kuma an kwantar da su a asibiti."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng