Buhari ya nada Kabiru Bala a matsayin babban kwamishinan Najeriya a Afrika ta Kudu

Buhari ya nada Kabiru Bala a matsayin babban kwamishinan Najeriya a Afrika ta Kudu

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada Ambasada Kabiru Bala a matsayin sabon babban kwamishinan Najeriya a jumhuriyar Afrika ta Kudu.

Ambasada Bala ya karbi wasikun shaidar nadin daga ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, cewar hadimarsa, Sarah Sanda.

Har zuwa lokacin sabon nadin nasa, Ambasada Bala wanda ya kasance mataimakin babban kwamishinan Najeriya a kasar Ingila.

Buhari ya nada Kabiru Bala a matsayin babban kwamishina a Afrika ta Kudu
Buhari ya nada Kabiru Bala a matsayin babban kwamishina a Afrika ta Kudu
Asali: Facebook

Ya shiga harkokin waje a 1999 sannan yayi aiki a Brasilia, Sudan, The Gambia, Netherlands da kuma Thailand.

KU KARANTA KUMA: Yan ta’addan Boko Haram sun kashe manoma 4 a Maiduguri

Legit.ng ta rahoto cewa Alhaji Ahmed Ibeto ya yi murabus daga matsayinsa a matsayin jakadan Najeriya a Afrika ta Kudu a watan Yuli 2018. Ya kuma koma jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) daga All Progressives Congress (APC).

Ibeto ya kasance mataimakin gwamnan jihar Niger na tsawon shekaru takwas, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shi a matsayin jakada sannan aka tura shi Afrika ta Kudu a 2016.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng