Kwamitin sasanci na APC ta sanya ranar fara zama
Kwamitin sasanci da kawo zaman lafiya wanda uwar jam’iyyar All Progressive Congress, (APC)ta kafa a yankin arewa maso gabas karkashin jagorancin Gwamnan jihar Nasarawa, Alhaji Tanko Alhamakura ta fara aikin da aka sanya ta.
A wani jawabi dauke da sa hannun sakataren kwamitin, Mohammed Hassan Abdullahi, Esq, ya ce “kwamitin za ta kai ziyara ga dukkanin mambobin am’iyyar a jihohin arewa maso gabas musamman wadanda suka gudanar da zaben fidda gwwani na jam’iyyar da aka kammala da kuma basu fafutuka a tsari da sakamkon zaben sannan ta tattauna da su.
“Hakan na daga cikin kokarin jam’iyyar na magance dukkanin lamura da rigingimu da suka taso a jam’iyyar sanadiyar zaben fidda gwani.”

Asali: Depositphotos
Sanarwar ta kuma kara da cewa an shirya tattaunawa a Yobe da Borno a ranar Talata, 27 ga watan Nuwamba a gidan gwamnati, Maiduguri da misalin karfe 12 na rana.
KU KARANTA KUMA: Zabe: Yan siyasa na kwasar dalibai a matsayin yan bangan siyasa – Sarki Sanusi
Sannan na Buachi da Gombe za su biyo baya a ranar Laraba, 28 ga watan Nuwamba a masaukin bakin Command, Awalah Roundabout, Bauchi da misalin 12 na rana.
Sannan Adamawa da Taraba a ranar Alhamis, 29 ga watan Nuwamba a gidan gwamnati, Yola, da misalin karfe 12 na rana.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng