Atiku da Sultan sun ba malaman Qur’ani wani babban aiki

Atiku da Sultan sun ba malaman Qur’ani wani babban aiki

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya yi kira ga cibiyar makaranta Qur’ani na Najeriya da su magance abunda ya kira a matsayin dodon rashin hadin kai a kasar.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi kiran ne a Sokoto a jiya Lahadi, 25 ga watan Nuwamba lokacin taron Alarammomi wanda kungiyar makaranta Qur’ani suka shirya a birnin Shehu.

Atiku wanda ya samu wakilcin hadimin labaransa, Suleiman Uba, ya ce shugabannin addini na da muhimmin rawar gani da za su iya takawa wajen wanzar da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin yan Najeriya.

Atiku da Sultan sun ba malaman Qur’ani wani babban aiki
Atiku da Sultan sun ba malaman Qur’ani wani babban aiki
Asali: Twitter

“Kasar mu ce gaba da komai. A yanzu haka, sai dai idan an dauki gagarumin mataki na kawo hadin kai idan bah aka ba abubuwa za su tabarbarewa ne."

Sultan na Sokoto, Alhaji Sa’ad Abubakar ya bukaci shugabannin malaman Qur’anin da su yi waje da malaman bogi wadanda ke hada koyarwar Islama da son zuciyarsu, kuma hakan kan kawo karshe mai muni da hatsari.

KU KARANTA KUMA: Kada ka ji komai za mu kawo maka kuri’u miliyan 15 – Kungiyar mata da matasan Arewa maso kudu

Mahaifan Aliko Dangote da Abdulsamad Isyaka Rabi’u na daga cikin wadanda aka karra a a wajen kan irin kokarin da suka yi wajen kawo ci gaba a hadin kan kasa ta hanyar koyarwar addini.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng