Hotunan yadda ake tsiren naman Kwado a Abuja
Kamar yadda kuma sani ba’a raba mutane da kayan makulashe musamman ma nama inda aka sarrafa ta nau’i daban-daban.
Sai dai wani labari da muka samu daga shafin BBC Hausa ya nuna cewa a yanzu abun har ya koma ga naman kwadi domin a yanzu haka an fara yin tsiren kwadin a babbar birnin tarayyar Najeriya, Abuja.
Wasu nauyin mutane dai sun dauki kwado a matsayin nama inda wasu suka ce yana karin jini da kuma lafiya.

Asali: UGC
Wani mai tsiren kwadin ya bayyana wa majiyarmu cewa suna saro kwadin daga Sabon Birni a jihar Sokoto sannan su kai Abuja suna sayarwa da jama’ar da ke da muradi.
Ya ce duk karamin tsinke ana sayar da shi naira 100, babba kuma naira 200 zuwa 250.

Asali: UGC
KU KARANTA KUMA: 2019: Gwamnoni sun lamunce ma Shugaba Buhari
Ana sarrafa shi a tsinke kamar yadda ake yin tsiren naman shanu ko kuma yadda ake jera kaji wajen gashi.
Ya ce a cikin mako daya suna iya sayar da tsinke 500.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng