Innalillahi wa inna ilaihi rajiun: Tsohon gwamnan Kaduna Abba Kyari ya rasu

Innalillahi wa inna ilaihi rajiun: Tsohon gwamnan Kaduna Abba Kyari ya rasu

Daga Allah muke, kuma gareshi zamu koma, don haka dukkani mai rai mamaci ne, Rahoton da muka samu da dumi dumi ya tabbatar da mutuwar tsohon gwamnan yankin Arewa ta tsakiya a zamanin mulkin Soja, Birgediya Abba Kyari, a daren Lahadi 25 ga watan Nuwamba.

Legit.com ta ruwaito wani ma’abocin kafar sadarwar zamani ta Facebook, kuma Da ga mamacin, Mohammed Kyari ne ya tabbatar da mutuwar mahaifin nasa ta shafinsa na Facebook, inda yace babansu ya mutu ne bayan doguwar jinya.

Innalillahi wa inna ilaihi rajiun: Tsohon gwamnan Kaduna Abba Kyari ya rasu
Innalillahi wa inna ilaihi rajiun: Tsohon gwamnan Kaduna Abba Kyari ya rasu
Asali: Facebook

KU KARANTA: 2019: PDP ta kalubalanci Buhari da ya zo su yi muhawarar ido-da-ido da Atiku

Shi dai Abba Kyari ya zama gwamnan Arewa ta tsakiya ne a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa na mulkin Soja, janar Yakubu Gowon, daga ranar 28 ga watan Mayu zuwa watan Yuli na shekarar 1975.

A shekarar 1967 ne janar Yakubu Gowon ya samar da jihohi goma sha biyu a Najeriya bayan ya rushe shiyyoyin Arewa da na Kudancin Najeriya, inda a cikin shiyya Arewa kadai sai daya samar da jihohi guda shida, daga cikinsu akwai jahar Arewa ta tsakiya, wanda daga bisani aka canja mata suna zuwa Kaduna a shekarar 1976.

Abba Kyari ya gaji tsohon gwamnan Arewa, Birgediya Hassan Usman Katsina, yadda abin ya faru kuwa shine a shekarar 1966 wasu kananan Sojoji yan kabilar Ibo suka yi juyin mulki ta hanyar kashe Sardauna Tafawa Balewa, shugaban shiyyar yammacin Najeriya da kuma sauran manyan Sojoji yan Arewa.

Innalillahi wa inna ilaihi rajiun: Tsohon gwamnan Kaduna Abba Kyari ya rasu
Innalillahi wa inna ilaihi rajiun: Tsohon gwamnan Kaduna Abba Kyari ya rasu
Asali: UGC

Sai dai duk da sunyi juyin mulki, basu samu nasarar kammalawa yadda ya kamata ba, sai babban hafsan Soja na wancan lokaci, Janar Agui Ironsi yah au karagar mulki, inda ya nada Hassan Usman Katsina a matsayin sabon gwamnan Arewacin Najeriya gaba daya.

Bayan wani dan lokaci, sai aka sake samun wasu Sojojin Arewa suka gudanar da juyin mulki, inda suka kashe Aguyi Ironsi, suka daura Janar Yakubu Gowon a matsayin sabon shugaban kasa, inda shi kuma ya nada Abba Kyari a matsayin gwamnan Arewa ta tsakiya, Kaduna.

Ana sa ran a yau ne iyalansa zasu bada karin bayani game da mutuwar tasa da kuma shirye shiryen yi masa jana’iza, Allah ya jikansa da gafara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: