Ku dena raki, ku tsige shugabanin da ba su tabuka komai ba - Abdulsalami ga matasan Najeriya
Tsohon shugaban kasan mulkin soji na Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar ya yi kira ga matasan Najeriya su tsige shugabanin da basu tabbuka komai a 2019 a maimakon su koma gefe suna ta korafi kan mawuyancin halin da kasar ke ciki.
Abubakar ya yi wannan jawabin ne a ranar Juma'a a Cibiyar koyar da dabaru da tsare-tsare da ke Kuru a Jos yayin wata lecture da aka shirya domin manyan ma'aikata da ke karatu a cibiyar su 40 inda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya hallarci taron a matsayin babban bako.
Tsohon shugaban kasar ya yi Allah-wadai da dabi'ar sayan kuri'u da wasu 'yan siyasa ke yi inda ya ce dole a hana wannan mummunan dabi'ar.

Asali: UGC
DUBA WANNAN: An kashe kuku bisa zarginsa da sata a gidan gwamna Dankwambo
Ya ce, "Kowanne dan Najeriya yana da nauyin da ya rataya a kansa. Bai kamata ku sayar da kuri'un ku ba. Ya zama dole kuyi rajista domin yin zabe.
"Ku dena bata lokaci kuna zagin gwamnati, kuna iya zuwa ku tsige su da kuri'un ku idan kana ganin wadanda kuka zaba ba su yin ayyukansu.
"Ya zama dole muyi kokarin kawo gyara a kasar mu ta hanyar bin doka. Ta haka ne kawai za mu iya samun shugabanci nagari a kasar.
"Ta wannan hanyar ne za mu gina cibiyoyi da za su tabbatar da adalci da gaskiya.
Kazalika, Abubakar ya soki yadda hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta yiwa jam'iyyu 91 rajista inda ya ce hakan ba zai taimakawa demokradiyar mu ba domin yawancin su ba su kafu da kafarsu ba kuma ba su da wata tsari ko alkibla.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng