Mutane 8 sun gurfana gaban Kuliya kan Satar N77m a jihar Ogun

Mutane 8 sun gurfana gaban Kuliya kan Satar N77m a jihar Ogun

A yau Juma'a mun samu cewa, wasu Mutane 8 sun gurfana gaban Kotun Majistire da ke garin Isabo a babban birnin Abeokuta na jihar Ogun, bisa aikata laifi na son banza inda suka yi awon gaba da N77m mallakin Ma'aikatar su.

Miyagun Mutanen 8 da hukumar 'yan sanda ta gurfanar a gaban Kuliya sun hadar da; Yusuf Azeez, Olausu Dauda, Olufunmi Falade, Olatunbosun Ogunseye, Samson Onabanjo, Abiodun Alonge, Moyindun Green da kuma Busura Habib da dukkanin su ke da shekaru na Matasa.

Jami'in dan sanda mai shigar da kara, Bukola Abolade, ya shaidawa kotun cewa ababen zargin sun aikata wannan mummunar ta'asa a tsakanin watan Janairu da Agusta a ma'aikatarsu ta Green Legacy Resort da ke garin Oke Mosan a birnin na Abeokuta.

Mutane 8 sun gurfana gaban Kuliya kan Satar N77m a jihar Ogun
Mutane 8 sun gurfana gaban Kuliya kan Satar N77m a jihar Ogun
Asali: UGC

Abolade ya shaidawa kotun cewa, ababen zargin sun yi tarayya da juna wajen kulla gami da makicin wawushe zunzurutun kudi na N77m mallakin ma'aikatar su.

Ko shakka ba bu wannan laifi na cin karo da sashe na 390 da kuma sashe na 516 cikin dokokin kasa kamar yadda jami'in dan sanda Abolade ya bayar da shaida gaban kotu.

KARANTA KUMA: Majalisar Dattawa ta fusata kan Mutuwar Dakarun Soji a Harin Boko Haram

Mai shari'a a wannan Kotu, Titilayo Bello, ta bayar da belin wannan miyagun Mutane kan makudan kudi na N2m ga kowanen su tare da daga sauraron karar zuwa ranar 8 ga watan Janairu kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, babbar Kotun jihar Zamfara ta karbe N120, 000 na cin tarar wani dan majalisar dokoki na jihar, Lawali Dogonkade, bisa aikata laifin zamba da rashawa ta N31.2m.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng