Yanzu Yanzu: Yan sanda sun tattara sun bar majalisar dokokin Akwa Ibom
Yan sanda sun kawo karshen mamayar da suka kai majalisar dokokin jihar Akwa Ibom.
Tun a safiyar ranar Talata, 20 ga watan Nuwamba dai aka yiwa kofar shiga majalisar kawanya.
Sai dai an bude a yanzu yayinda yan sanda suka tattara suka bar harabar majalisar a yau Juma’a, 23 ga watan Nuwamba.
A ranar Laraba ne dai jami’an yan sanda suka mamaye wajen bayan wani rikici da ya barke a ranar Litinin.

Asali: Depositphotos
Kakakin majalisar, Onofio Luke ya kaddamar da kujerun yan majalisa biyar da suka sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa All Progressives Congress (APC), a kasuwa, larin day a sa yan iska hargitsa majalisan.
Daga bisani sai yan sanda suka rufe majalisar suka hana yan majalisa da ma’aikata shiga majalisan.
KU KARANTA KUMA: Za mu sadaukar da rayuwar mu don al’umman mu – Yan bangan Zamfara
Jim kadan haka sai majalisar dattawa ta yi umurni kan a binciki dalilin rufe majalisar, bayan Sanara Bassey Akpan mai wakiltan Akwa Ibom ta Arewa maso gabas ya tayar da zancen .
Sannan kuma a ranar Alhamis sai majalisar dattawa ta umurci yan sanda da su yi gaggawan barin majalisan.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng